
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Kadarorin miliyoyin naira sun lalace sakamakon aukuwar wata ambaliya a yankin sanannen rukunin gidajen nan na Janar M.I. Wushishi (Mohammed Inuwa Wushishi) da ke garin Minna a Jihar Neja.
Haka kuma, ambaliyar ta haɗe wasu gidaje da ke rukunin gidajen, lamarin da ya tilasta wa mazauna yankin ɗebe kayayyakinsu daga cikin gidajen nasu.
Don haka waɗanda al’amarin ya shafa suka yi magiya ga gwamnati da ta kai musu ɗauki tare da warware matsalolin da ke haddasa ambaliya a yankin nasu.
Ɗaya daga waɗanda abin ya shafa mai suna Waziri Ahmed ya shaida wa manema labarai cewa ambaliyar ta lalata kusan komai a gidansa, waɗanda suka haɗa da kayan abinci, katifa, muhimman takardu da dabbobin da suke kiwatawa.
A cewarsa, ruwan da ambaliyar ta tara ya kai matakin ƙirjin mutum a tsaye, wanda ya sa mazauna suka riƙa ƙaura tare da ‘ya’yansu zuwa wurare masu aminci.
Akan haka ne Ahmed ya yi kira ga gwamnati da ta tallafa wa iyalan da iftila’in ya afka wa, waɗanda da damansu sun rasa kadarori masu yawa da matsugunansu.
Wata mai suna Bamidele Ajayi, ta ce ruwan ambaliyar ya cika mata gidanta kuma ya tafi da motarta da kusan dukkan abin da ta mallaka.
A cewarta, an shaida wa mazauna yankin cewa ayyukan haƙar ma’adinai ya taimaka wajen tare hanyar da ruwa ke bi ta yankin, lamarin da ya sa ruwa ke komawa wuraren da gidajen nasu suke da kuma haddasa ambaliyar, tana mai kira ga gwamnati da ta gaggauta ɗaukar matakan da suka dace wajen warware matsalar da kuma tallafa wa mutanen.
