Mutum 1,932 aka kashe cikin wata uku a Arewa maso Gabas – Majalisar Dinkin Duniya

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Hukumar Majalisar Dinkin Duniya Mai Kula da Daidaita Ayyukan Agaji (OCHA) ta bayyana cewa aƙalla mutum 1,932 ne suka rasa rayukansu a jihohin Borno, Adamawa da Yobe tsakanin watan Afrilu zuwa Yunin 2026, sakamakon matsalolin tsaro da suka addabi yankin.

Rahoton, wanda ya fito a ƙarƙashin Binciken Hanyar Isar da Agaji na Farkon Shekarar 2026, ya nuna cewa rashin tsaro, hare-hare kan ma’aikatan agaji da kayayyakinsu, cikas na hukumomi da kuma matsanancin yanayin muhalli ne suka fi kawo tsaiko ga ayyukan jinƙai a yankin.

Rahoton ya samo bayanansa ne daga ƙungiyar Aiki Kan Hanyar Isar da Agaji, tare da amfani da bayanan ACLED)da kuma Hukumar Majalisar ɗinkin Duniya Mai Yaƙi da Nakiyoyi (UNMAS).

Bayanan sun nuna cewa an samu aukuwar lamurra 60 da suka shafi abubuwan fashewa a cikin watanni ukun, ƙasa da 67 da aka samu a daidai wannan lokaci a shekarar 2025.

Haka kuma, hare-haren da aka yi da bama-baman ƙirar gida (IED) sun ragu daga 65 zuwa 54, yayin da yawan fararen hula da suka mutu ko jikkata sakamakon irin waɗannan hare-hare ya sauka daga 163 zuwa 54, abin da ke nuna raguwar kusan kashi 66.9 cikin ɗari.

OCHA ta danganta wannan sauƙi da ƙarin hare-haren haɗin gwiwa da Rundunar Sojin Nijeriya da sojojin Amurka suka ƙaddamar musamman a arewa da tsakiyar Jihar Borno, tare da cewa jama’a sun rage zirga-zirga saboda tsoron hare-hare.

Sai dai rahoton ya ce waɗannan farmakin soji sun haifar da ramuwar gayya daga ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai a yankunan Monguno, Damasak, Damboa, Bama, Konduga, Marte, Dikwa, Kukawa, Mobbar da Gwoza a Borno, da kuma Gujba a Yobe da Madagali a Adamawa.

Rahoton ya bayyana cewa hare-haren da aka kai sun tilasta wa ƙungiyoyin agaji dakatar da ayyukansu a wasu yankuna.

An dakatar da ayyukan kiwon lafiya da abinci mai gina jiki a Dapchi da ke ƙaramar Hukumar Bursari tun ranar 4 ga Afrilu bayan yawaitar hare-hare.

Haka kuma, ƙungiyoyin agaji sun dakatar da ayyukansu na ɗan lokaci a Madagali, yayin da aka rage ayyukan jin ƙai a Chibok bayan hare-haren da aka kai a farkon watan Afrilu.

Rahoton ya kuma ce sojojin Nijeriya sun samu nasarar fatattakar maharan da suka kai hari ƙauyen Bazamri da ke ƙaramar Hukumar Konduga ranar 13 ga Mayu, da kuma wani hari da aka kai madatsar ruwan Alou kusa da Maiduguri ranar 31 ga Mayu.

OCHA ta ce an gudanar da hare-haren sama guda 11 a Borno cikin wannan lokaci, inda mafi girma ya afku a Kasuwar Jilli, da ke kan iyakar ƙananan hukumomin Gubio da Geidam, ranar 12 ga Afrilu.

Sauran hare-haren sama kuwa sun fi mayar da hankali ne a Dajin Sambisa da kuma tsaunukan Mandara. Rahoton ya nuna cewa hare-haren da aka kai kan ma’aikatan agaji da motocin ɗaukar kayan tallafi sun ƙaru idan aka kwatanta da farkon shekarar.

A ranar 11 ga Afrilu, an kai hari tare da kwashe kayan wata motar da ke ɗauke da kayan agaji kusa da Gubio, yayin da ranar 24 ga Yuni aka sace ma’aikata biyu na wata ƙungiya mai zaman kanta a Monguno.

Haka kuma, ranar 29 ga Yuni sojoji sun daƙile wani hari da aka kai wa motar da ta kai kayan tallafi zuwa Damasak. Duk da haka, direban motar ya samu munanan raunuka bayan motar ta taka bom ɗin IED kusa da Kareto a ƙaramar Hukumar Mobbar.

Rahoton ya ce ambaliyar ruwa ta rushe wata gada a garin Rann ranar 18 ga Yuni, lamarin da ya ƙara wahalar da isar da kayan agaji.

An danganta hakan da hasashen Hukumar Kula da Yanayin ƙasa ta Nijeriya (NiMet) na shekarar 2026, wanda ya yi gargaɗin samun damina da wuri da kuma ruwan sama mai yawa.

OCHA ta kuma bayyana cewa matakan tsaro da sojoji suka ɗauka na hana safarar taki ba tare da izini ba domin hana ‘yan ta’adda ƙera bama-bamai sun janyo tsaiko ga aikin noma, musamman a lokacin da manoma ke shirin fara shuka.

Sai dai ta ce ta shiga tsakani domin samar da izinin da ya bai wa ƙungiyoyin agaji damar kai taki zuwa yankunan da ke da wahalar isa.

Rahoton ya ƙara da cewa, tashin farashin man fetur sakamakon rikicin da ya ɓarke tsakanin Amurka, Isra’ila da Iran ya ƙara tsadar jigilar kayan agaji.

Bugu da ƙari, a ranar 1 ga Yuni jami’an gwamnati sun tare wata motar da ke ɗauke da kayan agaji tare da buƙatar ƙarin takardun izini kafin su bari ta ci gaba da tafiya.

By ukarofi

Leave a Reply