
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Wani atisayen jami’an tsaro na haɗaka da rundunar sojoji ta jagoranta ya yi sanadiyyar sako baki ɗaya mutane 16 da wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a Ƙaramar Hukumar Ofu ta Jihar Kogi.
A ranar Lahadi, 9 ga Agusta 2026 ne aka sace mutanen bayan ‘yan bindigar sun farmaki mutanen da ke zirga-zirga a yankin titinan Ojuwo zuwa Ajengo zuwa Memarebo da Ojiwo zuwa Itobe.
Bayan samun wani bayanin sirri da ke nuna cewa an garzaya da mutanen ta yankin ƙauyen Adumu a Ƙaramar Hukumar Dekina, dakarun Bataliya ta 21 da haɗin-gwiwar jami’an sojojin ruwa na sansanin Lugard da ke Lokoja, rundunar ‘yan sanda, ‘yan bijilante da mafarauta, sun ƙaddamar da atisayen bincike da ceto.
A yayin haka ne suka yi nasarar cimma masu garkuwar da suka tsere da mutanen, lamarin da ya haifar da musayar wuta a tsakaninsu. A cewar sojoji, haɗakar jami’an ta yi galaba akan ‘yan bindigar wajen tilasta musu tserewa ɗauke da raunuka a jikkunansu.
Waɗanda aka ceto sun haɗa da maza shida, mata biyar da yara huɗu, waɗanda rundunar ta ce a yanzu haka ana duba lafiyarsu, inda ake sa ran haɗa su da iyalansu da zarar an kammala aikin.
Saidai, wani mafarauci ya rasu a yayin musayar wutar, yayin da wani jami’in ‘yan sanda ya samu raunuka, wanda yake karɓar magani.
Rundunar ta kuma yaba wa ƙoƙarin jami’an tsaro da masu ruwa da tsaki da suka taimaka wajen samun nasarar atisayen, tana mai cewa za ta cigaba da yaƙi da ayyukan garkuwa da mutane da ta’addanci a yankin da sauran sassan Nijeriya.
A ƙarshe, ta kirayi jama’a da su cigaba da kasancewa masu sanya ido tare da ruwaito wa hukumomin tsaro dukkan wani abin zargi da suka gani a yankinsu akan lokaci.
