Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Daracktocin hukumar tsaro na farin kaya na Arewa maso Yamma da ya ƙunshi jihohi 7 sun fara gudanar da taro a Katsina domin ƙara haɗin kai da ɓullo da shirin sabbin dabarun shawo kan matsalar tsaro a yankin.
A jawabin sa Gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Raɗɗa ya bayyana cewa matsalar tsaro da yadda ake tunkarar matsalar a jihohin Arewa maso Yamma yakamata ya zama bai ɗaya domin haka ya yaba wa hukumar DSS da sauka shirya wannan taro mai taken haɗa kai don yaƙar ta’addanci(United against Terror).
Gwamnan ya yaba wa da haɗin kai da goyon baya da hukumomi na tsaro da ke aiki a jihar da irin goyon baya da haɗin kai da suke bai wa gwamnatin jihar wajen yaƙi da ta’addanci.
Gwamnan wanda ya sami wakilcin mataimakin gwamna Faruk Lawal Joɓe,ya bayyana cewa lokacin da suka hau gwamnati, ƙananan hukumomi 26 da ke Jihar ke fama da matsalar tsaro.
“Kashe ƙarshen mutane,satar mutane don hamsar kuɗin fansa da sauran manyan laifuka sun zama ruwan dare a lokacin, amma ya zuwa yanzu zaman lafiya ya sami sanadiyar matakan da gwamnatin jihar ta dauka,”Inji Dikko Raɗɗa.
Ya ce jami’an tsaro a jihar sun san irin haɗin kai da goyon baya da mika bada wanda yasa zaman lafiya ya dawo a jihar, sai kuma muke taimaka wa iyalan mazajen da suka rasa rayukansu da waɗanda suka sami raunuka sakamakon hare haren ‘yan bindiga a Jihar.
Haka kuma Gwamnan ya bayyana ƙarin wasu matakai da gwamnati ta ɗauka da suka haɗa da bunƙasa tattalin arzikin Jihar ta fannin Noma, Ilimi,samar da aikin yi da kiwon lafiya.
Malam Dikko Raɗɗa ya yi kira da mahalarta taron da su sanar da gwamati abinda al’ummar ke buƙata daga gwamnati da zai taimaka ta ƙara ƙaimi wajen inganta tsaro a Jihar.
A Jawabin maraba daraktan hukumar a Katsina Alhaji A Iliasu ya ce yaƙi da ta’addanci ba wai ya tsaya a kan jami’an tsaro ba kawai ,ya shafi kowa shi yasa aka sama taken taron haɗa kai don yaƙi da ta’addanci.
Ya yaba wa gwamnatin Katsina akan irin matakai da ta ɗauka da yasa a yanzu aka sami gagarumin nasara a yaƙi da ta’addanci a Jihar.
Iliasu ya bayana cewa ana sa ran bayan taron hukumar za ta fito da wasu matakai da wasu tsare tsare da zai taimaka wajen kyautata tsaro a jihohin Arewa maso Yamma.
Taron ya sami halartar shugabannin hukumomi na tsaro a Jihar da suka haɗa da sojojin sama da na ƙasa , jami’an yan sanda, CWC,kwastan,shige da fice da sauran su.
Akwai tsaffin jami’an hukumar na DSS,da wakilcin sarakunan Katsina da Daura.
