Sanata Yar’adua ya yi na’am da komawar Mustapha Inuwa jam’iyyar APC a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Sanata Abdulaziz Musa Yar’adua mai wakiltar Katsina ta tsakiya a Majalisar Dattawa, ya bayyana farin cikinsa game da sauya shekar da tsohon sakataren gwamnatin Jihar Katsina, Dr. Mustapha Inuwa ya yi daga jam’iyyar African Democratic Congress, ADC, zuwa jam’iyyar All Progressives Congress, APC.

A wata sanarwara da ya fitar, Sanatan ya bayyana dawowar Dr. Mustapha a matsayin babban karin ƙarfi ga jam’iyyar APC da kuma alamar ƙaruwar amincewar al’umma ga gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Dikko Umaru Raɗɗa.

A cewarsa, “Na sami labarin dawowar babban ɗan’uwana, Dr. Mustapha Inuwa, zuwa jam’iyyar APC da matukar farin ciki, wannan abin alfahari ne ga jam’yyarmu ta APC da Dr. Mustapha ya dawo gida”.

“Dr. Mustapha jagora ne na gaskiya, gogaggen ɗan siyasa kuma mutum ne da ya san halin al’umma da siyasar Katsina. Ƙwarewarsa da ya samu a matsayin tsohon SGS zai taimaka matuƙa wajen ƙarfafa jam’iyyarmu da kuma kawo cigaba ga al’ummar Katsina ta Tsakiya da jiha baki ɗaya.” Inji shi.

Sanata Yar’adua ya ce komawar Dr. Inuwa zai ƙara haɗin kai da ƙarfin jam’iyyar APC a gabanin zaɓe mai zuwa, musamman a shiyyar Katsina ta tsakiya da ke da ƙananan hukumomi 11 da sauran ƙananan hukumomi 23 na shiyyoyin Funtua da Daura dake faɗin jihar.

Ya ƙara da cewa “Muna mashi barka da dawowa gida tare da duk magoya bayansa. Ina kuma rokon dukkanmu ‘ya’yan jam’iyyar APC da mu ba shi cikakken goyon baya, domin mu gudu tare mu tsira tare ta fuskar cigaba da kawo ayyukan alheri ga al’ummarmu.”

Dr. Mustapha Inuwa ya taba riƙe shugabancin jam’iyyar APC da kuma muƙamin sakataren gwamnatin Jihar Katsina daga 2015 zuwa 2023 a gwamnatin tsohon Gwamna Aminu Bello Masari. Kafin wannan canza shekar, ya kasance babban jagora a jam’iyyar ADC.

Masu nazarin siyasa na ganin wannan sauya sheka zai yi tasiri sosai a daidaiton siyasa ba kawai a shiyyar Katsina ta Tsakiya ba, a jihar baki ɗaya yayin da ake tunkarar zaɓen 2027.

By ukarofi