
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara akan Harkar Tsaro (NSA), Nuhu Ribaɗu ya jagoranci wata tawaga da gwamnatin Nijeriya ta shirya domin zuwa ƙasar Amurka halartar taron haɗaka tsakanin ƙasashen biyu, wanda aka gudanar a Birnin Washington D.C.
Zaman ya mayar da hankali ne akan haɗin kan lamuran daƙile ayyukan ta’addanci, nasarorin da aka samu zuwa yanzu da matakai na gaba da za ɗauka wajen ƙarfafa alaƙar tsaro tsakanin ƙasashen.
An gudanar da taro ne a ranar Alhamis, wanda kuma ya biyo bayan ayyana Nijeriya a matsayin ƙasar da ake damuwa akanta (CPC) da Amurka ta yi a baya.
Sauran waɗanda suka halarci taron tare da NSAn sun haɗa da:
“● Minister of Foreign Affairs, Bianca Odumegwu Ojukwu
●Minister of Defence, Christopher Musa
●Minister of Finance, Taiwo Oyedele
●Minister of Interior, Olubunmi Tunji Ojo
●Attorney General of the Federation, Lateef Fagbemi
●Minister of State for Foreign Affairs, Sola Enikanolaiye
●Chief of Defence Staff, General Olufemi Oluyede
●Nigeria’s Permanent Representative to the United Nations, Jimoh Ibrahim”, kamar yadda jaridar conclave ta ruwaito.
Allison Hooker ne ya jagoranci tawagar Amurka a ɗaya gefen, ƙarƙashin sakataren harkokin siyasar ƙasar.
Wannan taro wani matakin nasara ne na ƙarfafa haɗakar tsaron Nijeriya da Amurka da kuma haɗin kai akan lamuran tsaro.


