Daga RABIU SANUSI a Kano
Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya amince da aiwatar da sabon tsarin ƙarin albashi ga ma’aikatan koyarwa da waɗanda ba na koyarwa ba na Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Aliko Dangote da ke Wudil da Jami’ar Arewa maso Yamma ta Kano.
An ɗauko sabon tsarin ne daga tsarin albashin da Gwamnatin Tarayya ta fara aiwatarwa a jami’o’in tarayya. Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar ranar Litinin.
Amincewar ta biyo bayan rahoto da shawarwarin wani kwamiti da Majalisar Zartarwar Jihar Kano ta kafa domin nazari kan buƙatar jami’o’in biyu mallakin jihar na fara amfani da sabon tsarin albashin.
Bisa tsarin da aka amince da shi, sabon albashin zai fara aiki daga Janairun 2026, yayin da za a fara biyan kuɗin daga Satumbar 2026.
Jimillar kuɗin da sabon tsarin zai ci a kowane wata ga jami’o’in biyu ya kai Naira 391,847,555.24, wato Naira 4,702,170,662.88 a shekara.
A Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Aliko Dangote da ke Wudil, kuɗin da za a kashe a kowane wata ya kai Naira 228,195,210.83, inda Naira 141,082,223.37 za su kasance na malaman jami’a ƙarƙashin yarjejeniyar ASUU, yayin da Naira 87,112,987.46 za su kasance na ma’aikatan da ba na koyarwa ba ƙarƙashin SSANU.
A Jami’ar Arewa maso Yamma ta Kano kuwa, kuɗin da za a kashe a kowane wata ya kai Naira 163,652,344.41, wanda ya ƙunshi Naira 112,238,985.30 ga malaman jami’a da Naira 51,413,359.11 ga ma’aikatan da ba na koyarwa ba.
Gwamnatin jihar ta amince da saka Naira 1,567,390,220.96 cikin ƙarin kasafin kuɗin shekarar 2026 domin biyan kuɗin daga Satumba zuwa Disamba 2026.
Haka kuma, za a tanadi bashin albashin da ya taso daga Janairu zuwa Agusta 2026, wanda ya kai Naira 3,134,780,441.92, a cikin kasafin kuɗin shekarar 2027.
A cewar rahoton kwamitin, matakin na da nufin tabbatar da zaman lafiya a tsakanin ma’aikata da inganta jin daɗinsu, bisa tsarin da ake amfani da shi a jami’o’in tarayya da sauran jami’o’in jihohi.
Gwamna Yusuf ya kuma amince da duba yiwuwar kafa kwamitocin ziyara ga jami’o’in biyu da sauran manyan makarantun jihar, kamar yadda dokokin da suka dace suka tanada, domin ƙarfafa riƙon amana, inganta gudanarwa da tabbatar da ingantaccen shugabanci a cibiyoyin.
Gwamnan ya sake jaddada ƙudirin gwamnatinsa na inganta jin daɗin ma’aikata da ƙarfafa ingancin ilimin manyan makarantu a matsayin wani ɓangare na zuba jari wajen bunƙasa ilimin ɗan Adam.
