Daga MUAZU HARDAWA a Bauchi
Mazauna yankin Fego da Ruga Maikasuwa da ke ƙasar Gwana a ƙaramar Hukumar Alkaleri ta Jihar Bauchi, sun nemi taimakon gwamnatin jihar da hukumomin tsaro bayan ’yan bindiga sun kai musu hari a tsakiyar daren Asabar zuwa wayewar Lahadi.
Sheikh Yusuf Bello Gafaka, wani malami daga ƙasar Gwana, ya shaida wa wakilinmu a Bauchi cewa ’yan bindigar sun sake kai hari yankin ne kamar yadda suka yi a watannin baya, lamarin da ya tilasta wa wasu mazauna yankin yin hijira zuwa Jihar Gombe da wasu garuruwa domin tsira da rayukansu.
Ya ce bayan ɗaukar tsauraran matakai daga gwamnatin Jihar Bauchi da hukumomin tsaro, an samu raguwar matsalar tsaro, lamarin da ya ba mazauna yankin damar komawa garuruwansu tare da komawa gonakinsu.
Sai dai ya ce a daren Asabar, ’yan bindigar sun sake bayyana dauke da manyan makamai, inda suka afka wa garin Ruga Maikasuwa tare da raunata mutane shida, waɗanda a halin yanzu suke karɓar magani a wani asibiti da ke Gombe.
Sheikh Yusuf ya ce maharan sun kwashe shanun noma da wasu muhimman kayayyaki na mazauna yankin.
Ya ƙara da cewa ana ci gaba da bincike domin gano ko maharan sun tafi da wasu mutane, yana mai cewa mazauna yankin sun nuna jarumtaka tare da mayar da martani, lamarin da ya tilasta wa maharan tserewa bayan sun kwashe dabbobin da suka samu damar korawa.
Wakilin malaman Gwana, Sheikh Yusuf Bello Gafaka, ya kuma buƙaci gwamnatin jihar da hukumomin tsaro su gaggauta kawo musu ɗauki, yana mai cewa a halin yanzu babu isassun jami’an tsaro ko ƙwararrun ’yan sintiri a yankin tun bayan matakan da hukumomin tsaro suka ɗauka a baya domin dawo da zaman lafiya.
Yusuf Bello ya kuma buƙaci a kafa rundunar sojoji a yankin, musamman saboda yankin na maƙwabtaka da wasu jihohi biyar tare da kasancewa kusa da manyan dazuzzuka, ciki har da Yankari da makamantansu, waɗanda yake cewa ’yan bindiga na amfani da su wajen samun mafaka.
Da wakilinmu ya tuntubi kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bauchi, SP Nafiu Habib, domin jin ta bakinsa, ya ce bai samu rahoton harin ba a lokacin da aka tuntube shi.
Sai dai ya ce zai tuntubi DPO na Alkaleri domin samun cikakken bayani kan lamarin, sannan ya buƙaci a tura masa rahoto ga Kwamishinan ’Yan Sandan jihar domin ɗaukar matakan da suka dace da kuma ƙara tura jami’an tsaro yankin.
Ya ce matakan za su taimaka wajen kare rayukan mazauna yankin tare da ba su damar ci gaba da zama a garuruwansu cikin aminci.
