Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Sakataren Jam’iyyar ADC na ƙasa, kuma tsohon Gwamnan Jihar Osun, Rauf Aregbesola, ya bayyana cewa tun bayan da ya auri matarsa, Sherifat, bai taɓa yin wata alaƙar soyayya ko ta kusanci da wata mace ba.
Aregbesola ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi ga magoya bayan jam’iyyar ADC a wani gangamin yaƙin neman zaɓe da aka gudanar a ƙaramar Hukumar Ejigbo ta Jihar Osun, gabanin zaɓen gwamnan jihar da aka shirya gudanarwa a ranar 15 ga Agusta, 2026.
Tsohon gwamnan, wanda ya yi jawabin ne da harshen Yarbanci, ya ce tsoron Allah da kuma alƙawarin da ya ɗauka wa kansa su ne suka sa ya kasance mai aminci ga matarsa.
Ya ce, ya ɗauki wannan aminci a matsayin wani nau’in jarrabawa ga kansa a lokacin da yake neman taimakon Allah da kuma fatan samun nasara a burinsa na siyasa. A cewarsa, ya roƙi Allah da cewa idan da gaske yake bautarSa, kuma bai haɗa wani abu da bautar ba, to zai kasance mai gaskiya ga matarsa.
Aregbesola ya ce, “Saboda tsoron Allah, tun bayan da na auri matata ban taɓa yin kusanci da wata mace ba.”
Ya kuma bayyana cewa yana da burin ganin ya samu damar komawa gidan gwamnati a watan Yuni mai zuwa. Aregbesola ya riƙe matsayin Gwamnan Jihar Osun daga shekarar 2010 zuwa 2018, kuma a halin yanzu shi ne Sakataren Jam’iyyar ADC na ƙasa, wadda ke ƙalubalantar jam’iyyar mai mulki a zaɓen gwamnan Osun na bana.
Zaɓen gwamnan Jihar Osun na 2026 an shirya gudanar da shi ne ranar Asabar, 15 ga Agusta, 2026. Rahotanni sun nuna cewa an samu wasu tashe-tashen hankula na siyasa a jihar, inda rikice-rikice tsakanin magoya bayan jam’iyyun APC da Accord suka haddasa asarar rayuka.
Gwamna Ademola Adeleke na Jam’iyyar Accord na neman wa’adin mulki na biyu, yayin da Bola Oyebamiji ke neman kujerar gwamna a ƙarƙashin APC, yayin da Najeem Folasayo Salaam yake takarar ADC.
Yayin da zaɓen ke ƙara matsowa, jam’iyyar ADC ta ƙara zafafa yaƙin neman zaɓenta a sassa daban-daban na jihar, da nufin kwace mulki daga hannun gwamnatin da ke jagoranci a yanzu.
