Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Tsohon Shugaban ƙasar Nijeriya, Olusegun Obasanjo, ya soki tsarin dimukraɗiyyar da ake amfani da shi a yawancin ƙasashen Afirka, yana mai cewa tsarin dimukraɗiyyar sassaucin ra’ayi da aka gada daga ƙasashen Yamma bai dace da yanayin Afirka ba, kuma ya haifar da siyasar ‘mai nasara ya kwashe komai’.
Obasanjo ya bayyana hakan ne a ranar Talata, yayin taron tattaunawar dimukraɗiyya na gidauniyar tsohon Shugaban ƙasa Goodluck Jonathan na shekarar 2026, wanda aka gudanar a Bauchi, babban birnin Jihar Bauchi.
Tsohon shugaban ya ce tsarin dimukraɗiyyar Yamma da ƙasashen Afirka suka gada bai ginu kan tarihi, al’adu da yanayin zamantakewar nahiyar ba. Ya kwatanta amfani da tsarin da sanya tufafin da ba a auna mutum da su.
Ya ce, tsarin ya haifar da al’adar siyasa inda jam’iyyar da ta yi nasara a zaɓe ke kallon waɗanda suka sha kaye a matsayin abokan gaba, maimakon abokan hamayya masu kishin ƙasa. Obasanjo ya ce, a tsarin da ake bi yanzu, ko da ɗan takara ya samu ƙuri’a fiye da abokin hamayyarsa da ƙuri’a guda, zai iya karɓe dukkan madafun iko, yayin da ra’ayoyin sauran masu zaɓe ba su samun muhimmiyar kulawa.
“Dimukraɗiyyar da muke aiwatarwa ba ta da yanayin Afirka, ba ta da abin da ya dace da Afirka. Idan ka doke ni da ƙuri’a ɗaya, sai ka karɓe komai, abin da nake da shi kuma bai da wani tasiri,” inji shi.
Tsohon shugaban ya kuma nuna damuwa kan yadda ake tafiyar da bambancin addini, al’adu da ƙabilu a Nijeriya, yana gargaɗin cewa bai kamata tsarin dimukraɗiyya ya yi watsi da muhimmancin bambancin al’umma ba. Ya ce, bambancin jama’a shi ne ginshiƙin Nijeriya, don haka ya kamata a kula da shi tare da tabbatar da cewa yana zama abin haɗa kai, ba abin raba ƙasa ba.
“Nijeriya ita ce Nijeriya saboda bambancin da ke cikinta. Idan ka cire bambancin daga Nijeriya, za ka iya samun Jamhuriyar Oduduwa ko Jamhuriyar Dan Fodio, amma hakan ba zai sake zama Nijeriya ba. Dole ne a raya wannan bambanci kuma a kula da shi,” inji Obasanjo.
Obasanjo ya kuma soki yadda kuɗi da sauran hanyoyin sayen goyon baya ke ƙara samun gindin zama a siyasar Nijeriya. Ya ce, tasirin kuɗi da sauran nau’o’in abin da ake bayarwa domin samun goyon bayan siyasa na ƙaruwa cikin sauri, lamarin da ke barazana ga ingancin dimukraɗiyya.
Ya amince cewa, talauci da ƙarancin ilimi suna daga cikin matsalolin da ke kawo cikas ga ingantacciyar dimukraɗiyya, amma ya kuma nuna damuwa kan ƙarancin wakilcin mata a siyasar Nijeriya. Obasanjo ya ce tun bayan dawowar mulkin farar hula a Jamhuriya ta Hudu, sama da shekaru 24, Nijeriya ba ta samu mace a matsayin gwamna ba.
“Nijeriya na buƙatar tsarin siyasa da ya dace da tarihinta,” inji shi.
Da yake magana kan abin da ya kamata a yi, tsohon shugaban ya ce bai kamata Nijeriya ta dogara kawai da kwafin tsarin jam’iyyun siyasa da hukumomin shari’a daga ƙasashen Yamma ba.
Ya jaddada cewa, dimukraɗiyya ba wata manufa ce da ake kai wa a tsaya ba, illa dai tsari ne da ke buƙatar ci gaba da gyare-gyare. Ya ce, tun da ƙasashen da Afirka ta aro tsarin dimukraɗiyyar sassaucin ra’ayi daga gare su ma suna sake nazarin wasu ɓangarorin tsarin nasu, bai kamata Afirka ta ji tsoron sake duba nata tsarin ba.
“Ku kira shi da duk sunan da kuka ga dama, amma ku tabbatar yana da tarihi, al’adu da ƙimomin Afirka. Za ku iya kiransa dimukraɗiyya, ko kuma dimukraɗiyyar Afirka; amma dole ya kasance yana da yanayin Afirka da abin da ya dace da Afirka,” inji shi.
Taron, wanda Obasanjo ya jagoranta, ya samu halartar tsohon Shugaban ƙasa Goodluck Ebele Jonathan da tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa Namadi Sambo.
Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, ne ya karɓi baƙuncin taron, wanda kuma ya haɗa masana kan kundin tsarin mulki da masu fafutukar kare haƙƙin jama’a daga sassa daban-daban na nahiyar Afirka.
