‘Yan daba sun farmaki fadar basaraken Osun gabanin zaɓen gwamna

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

An zargi wasu ‘yan daba da kai farmaki a fadar Aree na Iree, Oba Muritala Oyelakin a ranar Juma’a yayin da ake ƙasa da sa’o’i 24 da fara zaɓen gwamnan Jihar Osun.

Al’amarin ya faru ne da misalin ƙarfe 2 na dare, wanda ya haifar da damuwa acikin al’umma kan tsaron masarautu da masu sarauta yayin zaɓen, wanda ke gudana a yau Asabar.

Basaraken, yayin ganawa da manema labarai a ranar Juma’a, ya ce maharan sun je fadar tasa ne a wasu motoci biyu masu ƙirar Sienna, inda suka yi harbe-harbe a sama kana daga bisani suka kusanci ƙofar fadar ɗauke da makamansu.

Ya bayyana cewa, al’amarin ya faru ne a lokacin da suke tsaka da gudanar da addu’o’i tare da wasu mutane a farfajiyar fadar.

A cewarsa, ta yiwu yawan mutanen da ke fadar ne ya hana maharan shiga ainihin harabarta, yana mai cewa mutane da dama suna farke a lokacin.

Ya ƙara da cewa, ya yi ta ƙoƙarin kunna fitilar hannu da kashewa domin tsorata su, inda mutane da dama suka yi cincirindo a fadar don hana maharan shiga.

Akan haka ne ya yi kira ga hukumomin tsaro da su gudanar da bincike akan al’amarin tare da kama dukkan masu hannu aciki don gurfanar da su su fuskanci hukuncin doka.

By Babaji

Leave a Reply