‘Yan sanda sun tabbatar da harin ‘yan ta’adda a Sakkwato

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Rundunar ‘Yan sanda a Jihar Sakkwato ta tabbatar da cewa wasu da ake zargin ‘yan ta’addan Lakurawa ne sun kai wani hari a garin Kebbe a ranar Juma’a, inda ta ce jami’an tsaro sun mayar da martani kuma an tura ƙarin wasu a yankin.

Haka kuma, rundunar ta ce babu wani farar hula da aka halaka ko jikkata harin saɓanin wasu rahotanni da ke nuna ‘yan ta’addar sun halaka mutane da dama.

Wasu rahotanni da aka wallafa bayan aukuwar lamarin sun bayyana cewa an halaka soja guda huɗu a yayin arangamar, amma Rundunar Soji ba ta tabbatar da adadin waɗanda suka rasu ba a lokacin da aka nemi ji ta bakinta.

Kakakin ‘yan sandan Sakkwato, Ahmad Rufa’i, ya ce wasu ‘yan ta’adda cikin adadin mai yawa sun afka wa garin Kebbe, wato hedikwatar Ƙaramar Hukumar Kebbe ta jihar a safiyar Juma’a, inda suka yi musayar wuta a tsakaninsu da jami’an tsaro. Ya ce, ‘yan sanda sun mayar ta martanin harin amma babu wani rashi ko jikkata da aka samu daga ɓangarensu.

Ya bayyana cewa, ya samu labari daga sojoji cewa wasu jami’ansu sun jikkata, saidai ba a bayyana ainihin adadin waɗanda suka rasu ko samun rauni ba a yayin harin kasancewar ba shi da ikon yin magana a madadin rundunar.

A yanzu dai ana jiran samun ƙarin bayani daga bakin rundunar sojojin kan halin da jami’an nasu suka samu kansu acikin yayin faruwar al’amarin.

By Babaji

Leave a Reply