Me ya sa wasu ‘ya’ya ke bijire wa iyayensu?

Spread the love

Daga MUKHTAR YAKUBU 

Tasirin rikicin iyaye ga ƙwaƙwalwar yara

Allah maɗaukakin Sarki ya ce:”Ya ku waɗanda suka yi imani! Ku tsare kanku da iyalanku daga wuta.” (Suratut-Taḥrīm: 6)

Iyaye da yawa suna tambaya: “Me ya sa ɗana ko ‘yata ba sa jin magana?” 

Ko kuma: “Me ya sa yaro yake da taurin kai?”

Sau da yawa ana kallon yaro ne kawai. Amma ilimin halayyar ɗan adam yana nuna cewa dole ne a kalli gidan da yaron ya taso kafin a yanke hukunci a kansa. ƙwaƙwalwar yaro tana gina kanta ne daga abin da take gani. Lokacin da yaro yake ƙarami, ƙwaƙwalwarsa tana koyon rayuwa ne ta hanyar kallon iyayensa.

Ba magana kawai yake ji ba. Yana kallon yadda suke magance matsala. Yana kallon yadda suke magana da juna. Yana kallon yadda suke nuna soyayya ko fushi.

Waɗannan abubuwa suna zama abin da ƙwaƙwalwarsa take ɗauka a matsayin hanyar rayuwa.

Me yake faruwa idan iyaye suna yawan samun rikici a tsakanin su?

Idan gida ya zama wajen hayaniya, zagi, cin mutunci, ko tashin hankali, ƙwaƙwalwar yaro tana rayuwa cikin yanayin faɗakarwa a kowane lokaci.

Masana ilimin ƙwaƙwalwa sun nuna cewa yawan fuskantar tsoro da rikici na iya sa yaro ya kasance cikin damuwa, ya kasa mai da hankali, ko ya rinka saurin fushi. 

Hakan kuma na iya shafar yadda yake koyon darasi, yadda yake sarrafa motsin zuciya, da yadda yake hulɗa da mutane.

Saboda haka, abin da ake kira “bijirewa” wani lokaci ba mugun hali ba ne. Yana iya zama martanin ƙwaƙwalwa ga yanayin da take ciki.

Yara suna koyon halayya fiye da umarni.

Idan uba yana gaya wa ɗansa kada ya yi fushi, amma shi kullum cikin fushi yake, yaron zai fi koyon fushin da yake gani fiye da kalmomin da yake ji daga bakin mahaifinsa.

Idan uwa tana koyar da gaskiya amma yaro yana ganin ana yin ƙarya a gida, abin da yake gani shi ne zai fi tasiri.

Shin kallon fina-finai yana da tasiri?

E, yana da tasiri sosai, musamman ga yara. ƙwaƙwalwar yaro ba koyaushe take iya bambance abin da ya dace da abin da bai dace ba. Abin da yake yawan gani yana iya zama abin koyi a gare shi. Idan yaro yana yawan kallon fina-finan da suke cike da: tashin hankali, cin mutunci, rashin kunya, ƙarya, ramuwar gayya, ko rashin biyayya ga iyaye, akwai yiwuwar ya fara ɗaukar waɗannan abubuwa a matsayin al’ada.

Haka kuma, idan yana kallon abubuwan da suke koyar da tausayi, gaskiya, ladabi, da kyawawan ɗabi’u, hakan na iya taimaka masa wajen gina halayya mai kyau.

Saboda haka, ba kallon fim kaɗai ba ne matsala. Abin da ake kallo, tsawon lokacin kallonsa, da kuma kulawar iyaye su ne suke da matuƙar tasiri.

Shi ya sa tarbiyya ba ta fara da gyaran yaro ba. Tana farawa ne da gyaran iyaye.

Saboda haka yaro yana iya mantawa da abin da ka faɗa masa. Amma yana da wuya ya manta da yadda ka sa ya ji.

Idan kullum yana rayuwa cikin tsoro, ƙasƙanci, ko rashin kwanciyar hankali, waɗannan abubuwa suna iya zama wani ɗangare na halayyarsa.

Me ya kamata iyaye su yi ?

Su rage rikici a gaban yara har ma da bayan idon su. Su rinƙa tattaunawa cikin mutunci idan aka sami sabani. Su rinka nuna ƙauna da girmamawa ga juna. Su rinka sauraron yaran kafin su hukunta su. Su zama abin koyi a cikin haƙuri, gaskiya, da tausayi. Yaro yana buƙatar gida mai aminci kafin ya buƙaci nasiha mai yawa.

Manzon Allah (SAW) ya kasance mai tausayi ga yara. Bai gina tarbiyya a kan tsoratar wa ba. Ya gina ta a kan rahama, adalci, da kyakkyawan misali.

Idan gida ya cika da rahama, yaro zai fi sauƙin karɓar tarbiyya. Idan gida ya cika da rikici, zuciyar yaro za ta yi wahalar samun nutsuwa.

Ba kowane yaro mai bijirewa ne yake ƙin iyayensa ba. Wani lokaci yana bayyana abin da ƙwaƙwalwarsa ta sha ne.

Kafin ka tambayi, “Me ya sa yaron nan ya canza?”

Ka fara tambayar, “Me yake gani? Me yake ji? Kuma wane yanayi yake rayuwa a cikinsa?”

Domin yara ba kawai suna jin maganar iyaye ba ne. Suna rayuwa ne da abin da iyayen suke yi.

Idan iyaye suka gina gida bisa soyayya, adalci, da natsuwa, sun riga sun kafa mafi ƙarfi daga cikin ginshiƙan tarbiyyar ɗansu.

Allah Ya sanya gidajenmu su zama gidajen rahama, Ya gyara zukatan iyaye da ‘ya’ya, Ya kuma ba mu hikimar tarbiyyar da za ta gina al’umma ta gari.

Mukhtar Yakubu

Dan jarida ne, mai nazarin al”amuran yau da kullum.

Ya rubuto ne daga garin Kano 070 30924846

By ukarofi

Leave a Reply