Daga RABIU SANUSI a Kano
Gwamnatin Jihar Kano ta yi watsi da wani rahoto da ƙungiyar Tracka ta wallafa, wanda ya yi zargin cewa an ware Naira miliyan 235.4 a cikin kasafin kuɗin shekarar 2025 domin gina ajujuwa a Government Girls Secondary School, Massu, da ke ƙaramar Hukumar Sumaila.
Gwamnatin ta bayyana rahoton a matsayin mai ɓatarwa kuma wanda ba shi da cikakkiyar hujja.
Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, Comrade Ibrahim Abdullahi Waiya, ya bayyana hakan ne ranar Laraba, 12 ga Agusta, 2026, yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a zauren taro na ma’aikatar da ke Kano.
Waiya ya ce zargin bai yi daidai da bayanan da ke cikin rahoton aiwatar da kasafin kuɗin jihar na zangon ƙarshe na shekarar 2025 ba.
Kwamishinan ya ce gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta ware Naira biliyan 168.35, wato kusan kashi 31 cikin 100 na kasafin kuɗin shekarar 2025, ga fannin ilimi.
Ya bayyana cewa kuɗaɗen sun taimaka wajen gyaran makarantun ’yan mata, ɗaukar malamai aiki, samar da kayan makaranta, inganta tsaro da kuma aiwatar da manyan ayyukan more rayuwa a fannin ilimi a ƙananan hukumomi 44 na jihar.
Waiya ya ƙalubalanci Tracka da ta gabatar da cikakkun hujjoji kan zargin, ciki har da shafin da lambar NCOA da aka ambata a rahoton kasafin kuɗin, takardar bayar da kwangila, takardar biyan kuɗi da kuma sunan ɗan kwangilar.
Ya kuma bayyana cewa Ma’aikatar Ilimi da Hukumar SUBEB na gudanar da binciken cikin gida kan ayyukan ilimi a Sumaila, inda ya ce za a fitar da sakamakon binciken ga jama’a.
Kwamishinan ya jaddada cewa babu wani aiki da aka bayyana da suna “GGSSS Massu, Sumaila – N235.4m” a cikin kasafin kuɗin shekarar 2025 ko kuma wasu amincewar Majalisar Zartarwar Jihar Kano da gwamnati ta gabatar.
Ya ce gwamnatin jihar za ta ci gaba da maraba da sahihin sa ido daga ƙungiyoyin fararen hula, amma ta bukaci duk wani rahoton bincike ya kasance bisa ingantattun hujjoji, domin kauce wa yaɗa bayanan da za su iya ruɗar da jama’a.
