
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Rikicin siyasa da ya dabaibaye jam’iyyar APC a Jihar Kwara ya ɗauki wani salo mai kama da wasan kwaikwayo yayin da Sanata Saliu Mustapha da ke wakiltar Kwara ta Tsakiya ya samu tikitin shiga takara a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar PDP domin neman kujerar sanatan yankin a zaɓen 2027.
Hakan na zuwa ne sa’o’i bayan sanatan ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar mai mulki a hukumance kan wata taƙaddama da Gwamna Abdulrahman AbdulRazaq da ake ganin ita ta sabbaba ɗaukar matakin nasa.
A ranar Juma’a Mustapha ya karɓi fom ɗin PDP don shiga takarar, wanda shugaban jam’iyyar na Kwara, Hon. Isa Adamu Baw ya gabatar masa.
Jami’an jam’iyyar sun shaida wa manema labarai cewa an miƙa wa Mustapha tikitin ne bayan tattaunawa da tsohon ɗan majalisa Moshood Mustapha, wanda da fari aka so ba wa tikitin don wakiltar jam’iyyar a zaɓen sanatan Kwara ta Tsakiya.
Wannan mataki ka iya haifar da gagarumar hamayya a mazaɓar, yayin da sanatan zai kara da gwamnan, wanda zai wakilci APC.
Sanata Mustapha ya yi murabus daga APC ne bayan watanni da rikicin cikin jam’iyyar biyo bayan zaɓen fidda gwanin ɗan takarar gwamna, wanda kakakin majalisar dokokin jihar, Yakubu Ɗanladi Salihu ya lashe.
