Daga JOHN D. WADA a Lafiya
Gimbiya Dr. Margaret Elayo kwamishiniyar ma’aikatar muhalli da albarkatun ƙasa kuma kwamishiniya mai riƙon kwarya na ma’aikatar harkokin mata da ayyukan jin ƙai a jihar Nasarawa ta raba buhunan shinkafa 600 a faɗin mazaɓu 10 na ƙaramar hukumar Keana a jihar Nasarawa.
Wannan tallafi ya kuma haɗa da rabon kuɗi domin ƙara wa tallafin abinci karfi. Wannan ya nuna jajircewar Dakta Elayo a matsayinta na mai fafutukar jin ƙai dake ƙoƙarin magance buƙatun al’ummar da ba su da ƙarfi.
Yanzu da ake fuskantar wani zaɓe Dr. Elayo tace jam’iyyar All Progressives Congress APC mai mulki za ta samu ƙarfi a jihar Nasarawa idan babu ƙarfi a jam’iyyar adawa. Saboda haka ta yi kira ga masu amfana da masu kaɗa ƙuri’a da su cigaba da riƙo da ƙa’idojin APC.
Taron rabon tallafin wanda kyauta ce ta kai tsaye daga kwamishiniyar muhallin Mr. Peter Ahemba mataimaki na musamman ga gwamna Abdullahi A. Sule kan harkokin yaɗa labarai ne ya wakilce ta a wajen rabon.
Masu amfana sun nuna farin cikinsu da karbar tallafin inda Hon. Ahemba ya sake jaddada jajircewar kwamishiniyar wajen cigaba da ayyukan jin ƙai kana ya buƙace su da su yi amfani da tallafin cikin hikima.
Wakilin mu a jihar ta Nasarawa yace kowane mai amfana ya samu buhu ɗaya na shinkafa mai nauyin kilogiram 10 da kuma Naira 5,000 inda aka kuma basu tabbacin cewa za a kawo ƙarin tallafin nan ba da daɗewa ba.
Hon. Ahemba ya buƙaci waɗanda ba su samu ba a wannan karon da su yi haƙuri. Yace kwamishiniyar a matsayinta na jagora a siyasance a Keana za ta cigaba da tallafa wa al’umma.
A ƙarshe sai ya kuma ja hankalin ‘yan APC da suka halarci taron da su haɗa kai domin tabbatar da nasarar dukkan ‘yan takarar APC a babban zaɓen 2027 mai zuwa wato daga ƙasa har sama.
