‘Ofishin Made in Nigeria halastacce ne’, inji Nwabueze yayin musanta zargin haramcinsa, ya fitar da shaidar bada aiki

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Kodineta na Ƙasa kuma Babban Daraktan ‘Ofishin National Brands Development and Made in Nigeria Special Project’ da ake taƙaddama a kai, George Nwabueze, ya musanta zargin cewa yana gudanar da “hukumar bogi” a Nijeriya.

Nwabueze ya bayyana haka ne ga manema labarai a ranar Asabar, inda ya ce ya jagoranci wani ofishi da ke gudana a ƙarƙashin sanya idon Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya (OSGF). Ya ce, ofishin yana aiki tun sawon shekaru 16 baya.

A ranar Juma’a ne Hukumar Yaƙi da Rashawa (ICPC) ta ce Shugaba Bola Tinubu ya umarci a kama Nwabueze bisa gudanar da hukumar, wadda ta ayyana a matsayin hukumar tarayya ta bogi. ICPC ta ce, wanda ake zargin yana gudanar da ofishin ne tare da haɗin-gwiwar manyan jami’an gwamnati a ofishin sakataren gwamnatin.

Saidai, yayin hira da wakilinmu, Nwabueze ya ce, “Ofishin ‘Made in Nigeria Special Project Office’ wani ofishi ne a OSGF a hukumance. Ba mu san inda aka samu hukumar bogi ba. Shirin da tun ranar 16 ga Yuli, 2010 yake sai jiya (Juma’a) aka gano. Bayan shekara 16; Nijeriya ƙasa ce mai abin dariya.”

Ya bayyana haka ne yayin amsa tambaya bayan ya wallafa takardar kama aiki a wani shafi, wadda ke ɗauke da kwanan wata 3 ga Oktoba, 2025, wadda kuma aka ce OSGF ne ya bayar da ita a hukumance.

Lambobin takardar sune OSGF/MIN/59310/11/205, wadda kuma ke ɗauke da sanya hannun Ofishin Babban Sakatare kan lamuran siyasa da tattali, Nadungu Gagare.

Kuma an gabatar da takardar shaidar ne kai tsaye ga “Hon. George Nwabueze, National Coordinator, Made in Nigeria Project Office, OSGF, Three Arms Zone, Abuja,” kuma ya karɓa kamar yadda ya yi iƙirari.

A cewar bayananta, naɗin na wa’adin shekara biyar ne, daga Juli, 2025 kuma za a iya sabuntawa. Haka kuma, takardar ta nuna cewa za a riƙa gudanar da harkokinta ne daga ɗaki na B53, gini na ƙasa a farfajiyar OSGF.

A yanzu dai ana dakon ji ta bakin OSGF da kuma ICPC kan iƙirarin Nwabueze game da al’amarin, wanda ya jefa al’umma cikin cece-kuce.

By Babaji

Leave a Reply