Al’ummar Dayi a Katsina sun yi taron inganta siyasa a garinsu

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Ƙungiyar cigaban Dayi mazauna Katsina sun yi taron masu ruwa da tsaki don bada gudunmuwa ta ingata rayuwar al’ummarsu ta Dayi da ke karamar hukumar Malumfashi.

A jawabin sa , shugaban ƙungiyar, mataimakin shugaban mai hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi na ƙasa mai ritaya Hamza Umar Dayi ya shaidawa mahalarta taron cewa an haɗu don a ingata siyasa ta mutanen garin Dayi.

Alhaji Hamza Umar Dayi ya tuno cewa babu wani lokacin da aka samu ɗan siyasa da ya taba wakiltar ƙaramar hukumar Malumfashi a majalisar jiha.

Yace yanzu jam’iyyar APC ta tsaida ɗan takarar majalisar jiha wanda zai wakilci ƙaramar hukumar Malumfashi daga garin Dayi.

Don haka, Alhaji Hamza Umar Dayi ya buƙaci ‘Ya’yan da su fito kwai da kwarkwata su mara mashi baya a zaɓen 2027.

A nasa jawabin a wajen taron, Alhaji Hassan Muhammad Tukur Dayi tsohon darakta a gidan Rediyo ya tunatar da mahalarta taron cewa can baya wani maƙwabcin garin watau Usman Na’alma ne ya wakilci ƙaramar hukumar Malumfashi a majalisar dokoki ta jiha.

Tun daga wancan lokacin, ‘yan siyasa daga Dayi basu samu damar tsayawa irin wannan takara sai a wannan lokacin.

Don haka Alhaji Hassan Muhammad Tukur Dayi ya buƙaci ‘yan ƙungiyar al’ummar Dayi mazauna Katsina da su fito su ga an kawo nasarar mataimakin shugaban ƙaramar hukumar Malumfashi Alhaji Muntari Adamu Dayi da ke takarar majalisar dokoki ta jiha.

A nasa jawabin, tsohon shugaban ƙaramar hukumar Malumfashi Alhaji Maharazu Adamu Dayi ya yabawa Alhaji Hamza Umar Dayi saboda kiran wannan taron don marawa Alhaji Muntari Adamu Dayi baya ya zama ɗan majalisar dokoki ta jiha mai wakiltar ƙaramar hukumar Malumfashi.

Alhaji Maharazu Adamu Dayi ya buƙaci a bunƙasa wannan goyon baya ya shiga lungu da saƙo na ƙaramar hukumar Malumfashi don samun nasara.

Da yake jawabinsa, Mataimakin Shugaban ƙaramar hukumar Malumfashi Alhaji Muntari Adamu Dayi kuma ɗan takarar majalisar dokoki ta jiha mai wakiltar ƙaramar hukumar Malumfashi ya nuna Jin daɗin sa da wannan taron da aka yi saboda neman nasara ga takarar da ya ke.
Alhaji Muntari Adamu Dayi ya gode wa Alhaji Hamza Umar Dayi da sauran ‘yan ƙungiyar al’ummar Dayi mazauna Katsina don nuna goyon baya.

Sauran waɗanda suka tofa albarkacin bakinsu a wurin taron sun haɗa da Sagir Hassan Dayi,Mutawakkil Hussain Dayi, Babangida Danyaro Dayi, Adamu Sha’aibu Gidanja Dayi,Aminu Abdullahi Dayi da sauran ‘yan kungiyar da dama.

By ukarofi

Leave a Reply