Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
An tsare babban dogarin Gwamnan Katsina (ADC) da kuma babban jami’in tsaron gwamnan (CSO) a hedikwatar ’yan sanda da kuma ta hukumar DSS da ke Abuja kamar yadda jaridar “Katsina Times ta bayyana.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa jami’an biyu suna hannun jami’an tsaro domin amsa tambayoyi.
Rahotanni sun ce lamarin ya samo asali ne bayan lalata wasu manyan allunan tallace-tallacen siyasa da ke kan hanyar shatale-talen Modoji zuwa gidan Gwamnatin Katsina. Wasu daga cikin allunan na ɗauke da hotunan shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da wasu manyan ’yan siyasa, ciki har da mai bai wa shugaban ƙasa Shawara kan harkokin Siyasa, Ibrahim Masari.
Bayan faruwar lamarin, an kai ƙorafi ga rundunar ’yan sanda da hukumar DSS, inda daga baya aka kama wani mutum mai suna Aminu Sanda, wanda aka fi sani da Aminu Nasta, wanda ake zargi da kasancewa shugaban wata ƙungiyar siyasa a Katsina.
Bisa bayanan da ake zargin jami’an tsaro suka samu yayin binciken, an gayyaci ADC da CSO na Gwamnan Katsina domin yi musu tambayoyi kan abin da suka sani game da lamarin ko kuma zargin cewa suna da alaƙa da waɗanda ake zargin sun lalata allunan.
Rahotanni sun kuma bayyana cewa shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin Katsina, Hon Abdulkadir Nasir, ya je Abuja domin ƙoƙarin ganin an sako jami’an.
Yayin da ake cewa har Gwamna Raɗɗa ma ya yi ƙoƙarin ganin an sake su, amma duk da haka ba a sake su ba suna tsare a Abuja.
