Tunanin Bahaushe game da zalunci: Nazari daga tatsuniyar iccen ƙosai

Spread the love

Daga SHEHU SANI LERE 

Gatanan-gatananku. Wani yaro ne ƙarami mahaifansa suka rasu suka bar shi a wajen ƙanin mahaifinsa, sun bar masa dukiya mai yawa. Sai ƙanin mahaifin ya hau kan dukiyar, sai ya zamo yana azabtar da shi. Ba a bashi isasshen abinci, sai dai kullum a bashi ƙosai ƙwara ɗaya, sauran yaran gida kuma a basu su ci su ƙoshi.

Ana anan, sai marayan nan ya shuka ƙosan da ake bashi yana zaga wa kullum yana bashi ruwa har ya tsiro ya zama bishiya babba, tayi ‘ya’yan ƙosai da yawa. Idan yaji yunwa, sai ya tafi wajen bishiyar ya yi mata waƙa kamar haka; “Sauko iccen maraya, sauko iccen ƙosai”.

Sai bishiyar ta rusuno ƙasa-ƙasa, sai ya hau yaci ya ƙoshi, sai ya ƙara yi masa waƙa ya ce; “Sama dai iccen maraya sama dai iccen ƙosai”. Lula iccen maraya lula iccen ƙosai.”

 Sai ya koma, sai ya dawo gida.

Kullum haka, kullum haka. Sai ƙanin mahaifinnan nasa ya yi ta mamakin yadda yaron nan yake ƙiba, alhali ba a bashi isasshen abinci.

Sai wata ran ya bi yaron a baya, ya laɓe don ya gano sirrin. Can sai yaji yaron na rera waƙa, sai icce ya sauko yaci ya ƙoshi.

Sai ya ce “to, koda naji”. Bayan yaron ya bar wajen, sai shima yaje ya rera waƙar, sai icce ya sauko, yaci ‘ya’yan ƙosai. Maimakon ya sauko, sai kawai ya rera, “Sama dai iccen maraya, sama dai iccen ƙosai”. Sai iccen ya yi sama-sama da shi, ya fyaɗo shi da ƙasa, ya karairaye.

Darasi:

A tunanin Bahaushe tun a gargajiyarsa kafin yasan wani abu addini, bai yarda da zalunci ba, hasali ma, yana ganin mummunar makoma ce ta dace ga duk wani azzalumi ko mai aikata zalunci.

To me ya sa, a yau masu addini, a wasu lokuta ma malamai basu ɗauki zalunci a bakin komai ba?

By ukarofi

Leave a Reply