Babban Sakataren NLC, Ugboaja ya rasu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Emmanuel Ugboaja, wanda shi ne Babban Sakataren Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa (NLC), ya rasu bayan shafe shekaru 60 a duniya.

An sanar da rasuwarsa ne yayin da ake tsaka da zaman kwamitin zartarwar NLC da aka gudanar a Inugu, ranar Alhamis. Shugaban ƙungiyar Joe Ajaero ne ya sanar da labarin ga mambobi kwamitin bayan karɓar wata wasiƙa daga iyalan marigayin.

A watan Agustan 2019 ne Ugboaja, wanda daɗaɗɗen ɗan ƙungiyar ƙwadago kuma lauya ne, ya zama babban sakataren NLC na biyar, inda ya gaji Peter Ozo-Eson a muƙamin.

Ya rasu ne bayan shafe tsawon lokaci yana jinya, sannan ya fara aiki a ƙungiyar ƙwadagon ne tun a 1993 bayan ya yi aiki a fannin shari’a mai zaman kansa.

Haka kuma, an haife shi ne a ranar 15 ga watan Mayu, 1966, kuma ya samu digirinsa na farko a Jami’ar Kalaba da ke Jihar Kuros-Riba a shekarar 1987. Daga bisani, ya shiga ƙungiyar National Union of Chemical, Footwear, Rubber, Leather and Non-Metallic Products Employees, inda ya riƙe muƙamin babban sakatare daga 2000 zuwa 2005.

Kazalika, ya kasance ɗaya daga cikin jiga-jigan ƙungiya da suka shiga sahun tattaunawa da jajircewa kan lamuran ƙwadago, aiwatar da mafi ƙarancin albashi da kuma walwalar ma’aikata a Nijeriya.

By Babaji

Leave a Reply