Daga UMAR GARBA a Katsina
Rashin jituwa da ke tsakanin Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umar Radda, da Hadimin Shugaban ƙasa, Ibrahim Masari, ya sa aka gayyaci jami’an tsaron Gwamna Radda zuwa Abuja.
Rikicin ya fara ne bayan da wasu matasa suka rushe wani babban allon siyasa da ke ɗauke da hoton Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.
Rahotanni sun bayyana cewa matasa ’yan bangar siyasa sun lalata allon sakamakon an sanya ɗan ƙaramin hoton Gwamna Radda, amma an sanya manya-manyan hotunan Shugaba Tinubu da kuma mai ba shi shawara kan harkokin siyasa, Ibrahim Masari.
An yi zargin cewa jami’an tsaron Gwamnan Jihar Katsina suna sane suka bari matasan suka lalata allon da ke tallata tazarcewar Shugaban ƙasa, wanda aka kafa a hanyar da ke zuwa Gidan Gwamnatin Katsina.
Wannan taƙaddama da ke tsakanin ɓangaren Ibrahim Masari da Dikko Umar Radda ana ganin ita ce ta sa aka gayyaci Dogarin Gwamnan Katsina, SP Abdulganiyu Bello, da kuma jami’in CSO.
Wasu rahotanni sun bayyana cewa yanzu haka DSP Hassan Bello yana can hedikwatar ’yan sanda a Abuja. An kira Dogarin tare da babban jami’in tsaron zuwa Abuja domin su amsa tambayoyi game da rusa allon da ke ɗauke da fastocin Shugaban ƙasa.
Manema labarai sun tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya, Anietie Iniedu, inda ya ce ba tsare waɗannan jami’an tsaro aka yi ba.
Kakakin ya musanta cewa Abdulganiyu Bello da Hassan Bello suna hannunsu tun ranar 20 ga watan Agusta, 2026.
An ce Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnatin Katsina, Abdulkadir Mamman Nasir, ya je Abuja domin ganin an saki waɗannan jami’ai, amma abin ya ci tura.
Bayanai da Blueprint Manhaja ta samu sun bayyana cewa ’yan sanda sun cafke wani ɗan siyasa, Aminu Sanda, bisa zargin cewa yana da hannu wajen lalata allon da ke ɗauke da fastocin Shugaban ƙasa da hadiminsa, Ibrahim Masari.
