Kungiyar ɗaliban Nijeriya ga Atiku: Dawo da tallafin fetur babbar matsala ne

Spread the love

*Ba mu da alaƙa da siyasa, inji Shugaban NAN

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Kungiyar ɗaliban Nijeriya ta ƙasa (NANS) ta soki ƙudirin tsohon Mataimakin Shugaban ƙasar Nijeriya, Alhaji Atiku Abubakar, na dawo da tallafin man fetur, tana mai cewa, hakan na iya sake jefa ƙasar cikin irin matsalolin tattalin arziki da tsarin tallafin ya haifar a baya ko ma fiye.

Shugaban NANS na ƙasa, Kwamared Akinteye Babatunde Afeez, ya ce, matsayar ƙungiyar ba ta da alaƙa da siyasa, sai dai ta samo asali ne daga abin da take ganin shine masalahar ƙasa.

A cikin wata sanarwa da ya fitar jiya, Afeez ya ce matsayar ɗalibai ba ta ginu kan goyon bayan wata jam’iyyar siyasa ba, illa dai kishin aasa da nazari kan abin da zai amfani Nijeriya.

Ya bayyana cewa NANS na da alhakin duba manufofin gwamnati cikin adalci tare da bayyana matsayarta kan muhimman batutuwan ƙasa, yana mai cewa nauyin ƙungiyar bai tsaya ga kare muradun ɗalibai kawai ba.

A cewarsa, babu shakka cire tallafin man fetur ya jefa ’yan Nijeriya cikin mawuyacin hali, musamman ganin yadda jama’a suka saba da fa’idodin da ake samu a ƙarƙashin tsarin. Sai dai ya ce nazarin yadda tattalin arzikin ƙasar ya kasance kafin da bayan cire tallafin ya nuna cewa akwai buƙatar yin garambawul.

“Duk ɗan ƙasa mai hankali kuma mai kishin ƙasa, wanda ya san halin tattalin arzikinmu, zai yarda da cewa cire tallafin man fetur ya kasance wani mataki mai wahala, amma dole ne a ɗauke shi domin gyaran tattalin arziki,” inji shi.

Afeez ya ce tsarin tallafin ya laƙume tiriliyoyin naira, inda masu yawan amfani da man fetur suka fi cin moriyarsa, tare da ƙarfafa safarar man fetur ta barauniyar hanya zuwa ƙasashen waje. Ya kuma ce tsarin ya takaita damar gwamnati na zuba jari a muhimman sassa na ƙasa.

Sai dai shugaban NANS ya amince cewa cire tallafin ya jawo tsadar man fetur, sufuri da kayan abinci a ɗan gajeren lokaci, lamarin da ya ƙara wa ’yan Nijeriya nauyin rayuwa. Amma ya ce matakin ya kuma samar wa gwamnati ƙarin damar kashe kuɗaɗe a wasu fannoni, tare da rage abin da ya kira babban karkacewar tattalin arziki.

A cewarsa, bai kamata a auna nasarar gyaran tattalin arzikin da irin kuɗin da gwamnati ta tara kawai ba, sai dai da yadda aka yi amfani da kuɗin wajen inganta rayuwar jama’a.

“Ainihin abin da ya kamata a auna nasarar wannan gyara da shi ba wai kuɗin da aka tanada kawai ba ne, amma abin da gwamnati za ta yi da waɗannan kuɗaɗen,” inji shi.

Saboda haka, Afeez ya yi watsi da kiraye-kirayen da ake yi na dawo da tallafin man fetur gaba ɗaya, muddin babu cikakken tsari da zai magance matsalolin da suka sa tsarin ya zama mara ɗorewa tun farko.

Ya ce, dawo da tallafin ba tare da wani sabon tsarin da zai magance waɗannan matsaloli ba, zai iya zama martanin siyasa ne kawai ga wata babbar matsalar tattalin arziki.

Shugaban NANS ya kuma yi kira ga ’yan Nijeriya da kada tsananin wahalhalun da aka fuskanta a sakamakon sauye-sauyen tattalin arziki ya sa a yi watsi da buƙatar sake fasalin tattalin arzikin ƙasa na dogon lokaci.

Ya buƙaci gwamnati da ta tabbatar da cewa an yi amfani da kuɗaɗen da aka samu sakamakon cire tallafin cikin gaskiya da tsanaki, musamman wajen inganta rayuwar ’yan Nijeriya, domin sadaukarwar da jama’a ke yi a yanzu ta haifar da alheri a nan gaba.

By ukarofi