Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta fara ɗaukar matakan farfaɗo da ayyukan binciken haƙo ɗanyen man fetur a Filin Mai na Kolmani da ke Jihar Bauchi, bayan da Hukumar Tattara Kuɗaɗen ƙasa da Rarraba Su (RMAFC) ta fara tantance halin da aikin yake ciki domin gano matakan da suka dace don sake dawo da shi.
Shugaban RMAFC, Muhammad Bello, ne ya bayyana hakan a ranar Litinin yayin wata ziyarar tantancewa da hukumar ta kai filin mai na Kolmani. Bello ya ce hukumar za ta duba yadda aikin yake a halin yanzu, tare da gabatar da shawarwarin da za su taimaka wajen ganin an dawo da ayyukan binciken man fetur a yankin.
Ya jaddada cewa farfaɗo da aikin Kolmani ba wai Jihar Bauchi da yankin Arewa maso Gabas kaɗai zai amfani ba, har ma yana da muhimmanci ga faɗaɗa tattalin arzikin Nijeriya baki ɗaya. Ya ce, “Muna son dawo da ƙwarin gwiwar aikin da aka fara a shekarar 2023. Mun zo ne domin mu gani da kanmu abin da ke faruwa, ta yadda za mu iya ba da shawarar a ci gaba da wannan muhimmin aiki, domin al’ummar Arewa maso Gabas su ƙara cin gajiyarsa.”
Shugaban RMAFC ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu na ci gaba da nuna damuwa da sha’awar ganin an farfaɗo da aikin Kolmani. Ya ce shugaban ƙasar ya tabbatar wa gwamnonin Bauchi da Gombe cewa za a yi ƙoƙarin sake tura ma’aikata da kayan aiki zuwa wurin domin ci gaba da ayyukan binciken mai.
“Mun san cewa Mai Girma Shugaban ƙasa yana matuƙar damuwa da wannan aiki. Mun kuma san cewa ya tabbatar wa gwamnonin jihohin biyu cewa za a sake tattaro kayan aiki da ma’aikata domin a ci gaba da aikin,” inji shi.
Bello ya bayyana cewa bayan kammala tantance aikin, RMAFC za ta gabatar da rahotonta ga hukumomin da abin ya shafa, sannan ta ci gaba da bibiyar ci gaban aikin ta hannun kwamitinta mai kula da harkokin mai da iskar gas. Ya ce hukumar za ta fara ne da tantance irin aikin da ake yi a Kolmani da kuma dalilan da suka jawo tsaiko, kafin ta gabatar da matakan da suka dace.
ƙoƙarin farfaɗo da aikin ya biyo bayan dakatar da ayyukan binciken mai a wurin, inda gwamnatin Jihar Bauchi ta tabbatar da cewa aikin ya tsaya ne a kusan watan Yulin 2025.
Kwamishinan Ma’adanai na Jihar Bauchi, Maiwada Bello, ya ce gwamnatin jihar ta fara samun labarin dakatarwar ne bayan al’ummar yankin da aikin yake suka sanar da ita cewa kamfanin fasaha da ke gudanar da aikin na kwashe kayan aikinsa daga wurin. Ya ce a lokacin da gwamnatin jihar ta kai ziyara wurin, babu wani aiki da ake gudanarwa. A cewarsa, daga farkon shekarar 2025 zuwa kusan watan Yuni ko Yulin wannan shekarar ne aka samu rahoton cewa kamfanin da ke gudanar da aikin ya fara ficewa daga wurin. Ya ce hakan ya sa gwamnatin jihar da ƙaramar hukumar da aikin yake suka kafa tawaga ta haɗin gwiwa domin tattaunawa da kamfanin fasaha da ke kula da aikin tare da gano matsalar.
Kwamishinan ya ce ziyarar RMAFC ta sake farfaɗo da fata cewa za a iya dawo da ayyukan binciken man a Kolmani. Ya tabbatar da cewa gwamnatin Jihar Bauchi a shirye take ta samar da ma’aikata da sauran tallafin da ake buƙata domin taimaka wa aikin ya koma kan turba. “Jihar Bauchi, ƙarƙashin jagorancin Gwamna Bala Mohammed, a shirye take ta samar da dukkan ma’aikatan da ake buƙata domin tallafa wa aikin binciken,” inji shi.
Aikin Kolmani na ɗaya daga cikin manyan ayyukan da ake ganin za su iya kawo sauyi ga tattalin arzikin yankin Arewa maso Gabas, musamman idan binciken ya tabbatar da cewa akwai ɗanyen mai mai yawa da za a iya hako shi cikin riba.
Idan aka tabbatar da samun man fetur mai amfani a kasuwanci, ana sa ran aikin zai samar da guraben ayyukan yi, buɗe damar ayyukan fasaha da ƙwarewa, tare da haifar da wasu harkokin kasuwanci da tattalin arziki a yankin.
