
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Rundunar ‘Yan sanda a Jihar Zamfara, ta tabbatar da harin ‘yan bindiga a babban titin Gusau zuwa Funtua da ke yankin Ƙaramar Hukumar Tsafe, sannan jami’anta sun ceto mutane guda tara da maharan suka yi yunƙurin sace su.
Haka kuma, ‘yan sandan sun cafko wani da ake zargi da safarar makamai da ƙwato wasu bindigogin gargajiya ƙirar AK-47 a wani atisayen daban a babban titin.
Al’amarin ya auku ne a ranar 28 ga Agusta, a cewar sanarwar da Kakakin ‘yan sandan, DSP Yazid Abubakar ya fitar. Ya ce, hakan ya samo asali ne da misalin ƙarfe 1:20 na rana a lokacin da babban ofishin ‘yan sandan tsafe ya samu kiran gaggawa kan rahotannin harbe-harben bindiga a yankin Kwanoni zuwa Gidan Giye na babbar hanyar.
Sanarwar ta bayyana cewa, ‘yan bindigar sun tare motoci guda biyu tare da farmakar mutanen da suke cikinsu. Ɗaya daga cikin motocin Sharon ce mai lambar KWL 742 ZY, wadda wani Lawal Dauda na Ƙaramar Hukumar Zariya ta Jihar Kaduna yake tuƙawa a lokacin da motar ke ɗauke da fasinjoji bakwai. Mota ta biyu kuwa ba ta da rajista, wadda wani mai suna Haruna Alhaji Nasiru na Ƙaramar Hukumar Ɗanja ta Jihar Katsina yake janta tare da ɗansa Sanusi Haruna bayan sun yi jigilar busassar rogo daga Funtua.
A cewar ‘yan sandan, DPOn Tsafe tare da wasu jami’an Sashen kula da Laifukan Tarzoma (VCRU) da wasu sojojin na ƙarƙashin Atisayen FANSAN YAMMA suka gaggauta zuwa wajen bayan samun kiran gaggawar.
A yayin haka ne dakarun suka yi arangama da ‘yan bindigar, inda suka nuna musu fin ƙarfi, lamarin da ya tilasta musu tserewa zuwa yankunan tsaunuka da ke bayan garin Tsafe. Bayan haka ne suka ceto baki ɗaya mutane taran ba tare da wata cutarwa ba.
A wani labarin kuwa a ranar da misalin ƙarfe 5:30 na yamma, jami’an VCRU sun kama wani ɗan shekara 50 mai suna Khalid Umar bisa zargin sa da safarar bindiga ƙirar AK-47 guda 11. Umar dai ɗan asalin ƙauyen Ganga na Ƙaramar Hukumar Tsafe ne, wanda aka cafke a babban titin Funtua zuwa Tsafe bayan samun wani bayani na sirri.
Bincike ya nuna cewa ana zargin mutumin ne da jigilar muggan makamai daga ƙauyen Shuwaki a Ƙaramar Hukumar Bakorin jihar Katsina zuwa Bawa Ganga a Zamfara.
