Daga ALI ABUBAKAR SADIQ
Wannan matsala, kamar sauran duk matsaloli da ke kawo cece-kuce a musulunci ba sabuwar matsala ba ce, domin ta faro akalla tun lokacin tabi’ai. Kamar sauran matsaloli za ka samu cewa akasari watsi da cikakkiyar koyarwa ta Qur’ani ke kawo su. Musulunci ya fara samun matsaloli tun bayan rasuwar annabi, sakamakon rarrabuwar kawuna da siyasa ta bijiro da su sakamakon halifanci, kuma wannan banbanci sannu a hankali sai ya tashi daga siyasa ya koma akida, abinda ya haifar da akidojin shi’anci, Kharijawa da Yan sunna da sauransu. Hakan ya haifar da kirkire-kirkire na hadisai wajen kokarin kare akidoji ko manufofi don samun nasarar wannan bangare a kan wancan. Wannan ya sa ake samun sabani a kan matsaloli.
Kafin duba maudu’in cewa shin iyayen Annabi na wuta ko a’a, abinda ya fara kamata mu yi shine fahimtar mai Allah cikin Qur’ani ya tarbiyantar da mu game da irin wadannan matsaloli. Duk wata al’umma da ta sami sakon shiriya, a kan samu cewa wasu cikinta na tambayar makomar mutanen wannan al’umma da su ka shude kafin zuwan wannan sako, kamar yadda Allah ya bamu labari cikin suratul Taha inda Fir’auna ke tambayar Musa: Q20:51-52 “Ya ce “To menene halin karnonin farko? Ya ce “Saninsu ya na wurin Ubangiji na, ubangijina ba ya kure kuma ba ya mantuwa.”
Kai tsaye Allah bai ce su na wuta ko a’a ba, sannan bai ce Musa na da hurumin fadar haka ba duk da cewa wadanda Fir’aunan ke tambaya a kansu kafirai ne, amma Allah ya nuna cewa amsar tambayar ba ta shafe ku ba, ya na sane da duk wani mai imani ko akasin haka, wato shi ya san dan wuta ko akasin haka. Duk da cewa Allah ya fadi sifofin yan wuta, amma wajibi sai bayan an mutu, an je kiyama an yi hisabi sannan za’a san wanene dan wuta.
Wannan sharadi da Allah ya dora kan Musa, irinsa dai ya dora kan Annabi Muhammadu inda ya ce cikin Suratul Baqara: Q2:119 “Lallai mun aike ka da gaskiya, ka na mai bayar da bushara, kuma mai gargadi, kuma ba za’a tambayeka ba, game da abokan wuta.”
Aikin da Allah ya aiko manzo shine yayi busharar shiga Aljanna ga masu imani da yin gargadin shiga wuta ga kafirai, amma waye Dan wuta ba huruminsa ba ne, na Allah ne shi kadai. Wadannan ayoyi sun nuna karara cewa annabawa ba su da hurumin cewa wane dan wuta ne.
Idan muka koma kan maudu’in, Allah ya kafawa kansa sharadin cewa: Q17:15 “…Kuma ba mu zama masu yin azaba ba, sai mun aika wani manzo.”
Don haka idan al’umma ba ta sami manzanci ba, Allah baya jefa mutanenta a wuta, amma kuma abin dubawa shine tsakanin wani Annabi kafin wani Annabi, misali idan mu ka yi la’akari da mutanen da su ka rayu bayan annabi Isa kafin zuwan annabi Muhammadu, shin wane aji za’a saka su? Hanifawa ne ko kuwa kafirai ne? Mun san dai shi kansa Annabi Muhammadu kafin ya kai shekara 40 ya na cikin Hanifawa tunda bai taba yin bautar gumakan Makka ba, shin iyayensa ma hanifawa ne ko kuwa akwai hujja cikakkiya cewa sun yi bautar gumakan Makka?
Shi Abdullahi Bn Abdulmutallib, tarihi ya tabbatar da cewa ya tafi Gaza cinikayya a karkashin ayarin Quraishawa, amma a hanyar dawowarsu daf da isowa Madina sai ciwon ajali ya kama shi don haka dole ya yada zango a Madina wurin yan uwan mahaifiyarsa Banu Adi b. al-Najjar da ke cikin kabilar Khazraj. An ce ya yi wata guda ya na jiyya kafin rai ya yi halinsa kuma aka binne shi a al-Nabigha (da ke yammacin inda masallacin Annabi ya ke a yanzu). A wannan lokaci, Amina na dauke da cikin Annabi. Ita kuma Amina tarihi ya tabbatar da mutuwar ta shekaru shida da mutuwar mijinta bayan ta dawo daga ganin gida a Madina kafin ta isa Makka a wani gari da ake kira Al-Abwa inda aka binne ta. Kafin ka ce iyayen annabi na wuta akwai bukatar tabbatar da kafircinsu, wanda babu tabbacinsa a tarihance.
Amma a kokarin lallai sai an tura iyayen Annabi cikin wuta sai ga hadisi ya zo daga Muslim cewa: “Wani mutum (ya tambayi Manzon Allah): ‘Ya manzon Allah, ina mahaifina ya ke yanzu? Sai Annabi ya ce masa: ‘Ya na Wuta’. Bayan mutumin ya juya ya tafi, sai annabi ya kira shi ya ce masa: ‘Da babana da babanka duk su na wuta (inna abī wa-abāka fī n-nār)’.”
Amma fa Muslim kadai cikin maruwaita ya kawo wannan hadisi, amma Bukhari, wanda duniyar sunni ta daukaka a matsayin daga Qur’ani sai shi a sahihanci, bai kawo wannan hadisi ba, me ya sa? Mun san cewa Bukhari ya tattaro hadisai da sun kai 600,000, aikin da ya fara tun yana dan karamin yaro mai shekaru 16. Amma a cikin tulin wadannan hadisai, da ya dinga tankade da rairaya, sai da ya rairaye hadisai 597,398 wadanda bai yarda da sahihancinsu ba (watakila a ciki har da wancan hadisi da Muslim ya kawo cewa iyayen annabi na wuta), inda ya dauki hadisai 2602 kacal, wato kasa da kaso daya 1% cikin kashi 100% na ilahirin hadisan da ya tattara. Wannan aiki na Bukhari kadai ya isa ya nuna mana irin tarin hadisai na karya da ke kara-kaina tsakanin al’ummar musulmi a karni na biyu lokacin da Bukhari ya yi aikinsa bayan wafatin manzon Allah.
Ziyarar da annabi ya kai kabarin mahaifiyarsa a shekara ta 6 bayan hijira shi ma ya kara rura wutar rikicin tsakanin masu ra’ayin iyayen nasa na wuta ko a’a. Wadanda ke sukar cewa iyayensa na wuta su na kafa hujja da wannan ziyara cewa da yan wuta ne ai da bai je kabarinta ya yi mata addu’a ba, tunda Allah ya hane shi yi wa kafirai addua a wannan aya: Q9:80 “Kõ kã nẽma musu gãfara ko ba ka nẽma musu ba, idan ka nẽma musu gãfara sau saba’in, to, Allah bã zai gãfarta musu ba. Sabõda sũ, sun kãfirta da Allah da ManzonSa. Kuma Allah ba Ya shiryar da mutãne fasikai.”
Sai daya bangaren ke cewa ai dalilin wannan ziyara kabarinta shine kuma Allah ya saukar da: Q9:113 “Ba ya kasancewa ga annabi da wadanda su ka yi imani, su yi istigfari ga mushrikai, kuma ko da sun kasance ma’abuta zumunta ne daga bayan sun bayyana a gare su cewa lallai ne su yan Jahim ne.”
Abin lura a nan shine, ya tabbata dai ya je ziyara kabarin nata amma kuma ayoyin Tauba sai a shekara 630 AD aka saukar da su bayan dawowa daga Tabuk ko a hanya. Kaga ayoyin ba za ka iya jingina su da ziyarar kabarinta ba domin akwai yan shekaru tsakani.
Rigimar ta lafa kafin wanzuwar Wahabiyanci a Saudi Arabia, amma zuwan Abdulwahab da kokarinsa na hana ziyarar kaburbura ya sake dawo da wannan tsohuwar muhawara sabuwa domin a shekarar 1930 karkashin gidan dab’in Salafiyya Press da ke Makka sun lalubo asalin sharhin Al-Qari game da fatawar cikin Fiqh al-akbar II suka buga shi aka watsa (sannan an sake buga shi a Madina a shekarar 1993 da gabatarwa Hassan Ibn Salman wanda ya yabi kokarin Al-Qari wajen kare fatawar cewa iyayen annabi na wuta). Haka nan jami’ar Ummul Qura da ke Makka ta saka wata makala cikin mujallarta wadda ke na’am da fatawar cewa iyayen annabi na wuta. A yayin da Salafawa ke sake rura wutar, sai kuma mabiya sufaye yan darikar Azmiyya a Misra ciki shekarar 2010 su ka gabatar da maulidin Amina, a kokarin sufantar da ita ko? Maulidin da har wasu manyan malaman jami’ar Azhar sun halarta. Kafin nan a shekarar 2007 Dar al-Ifta da ke da yawun Muftin Misra ta fitar da sanarwa cewa duk wanda ya ce iyayen annabi ba musulmi ba ne ya aikata babban zunubi.
A shekarar 1998 an gano wani kabari a kauyen al-Hurayba wajen da ake kyautata zaton cewa tsohon garin Al-Abwa ne, wanda ake zaton kabarin Amina ne. Nan da nan sai ma’aikatar kula da addini ta Saudi Arabia ta tura, cikin gaggawa da katafila taje ta baje kabarin kuma aka watsa fetur aka kone wajen gaba daya.
A takaice, maimakon yin amfani da fatawar Qur’ani cewa; Q20:51-52 “Ya ce “To menene halin karnonin farko? Ya ce “Saninsu ya na wurin Ubangiji na, ubangijina ba ya kure kuma ba ya mantuwa.”
Da kuma; Q2:119 “Lallai mun aike ka da gaskiya, ka na mai bayar da bushara, kuma mai gargadi, kuma ba za’a tambayeka ba, game da abokan wuta.”
An wayi gari an kirkiri hadisai na karya da ke ci gaba da raba kan musulmi: cewa annabi ya ce iyayensa na wuta da wanda ke cewa mahaifiyarsa ta tashi daga kabari ta yi imani da shi….to amma abinda makirkiran wannan hadisi su ka manta shine ba su ce ya je kabarin Abdullahi shi ma ya tashe shi ba, ko shi ba komai idan ya ci gaba da zama a wuta? Ko dai annabi mahaifiyarsa kawai ya damu da tsiranta banda mahaifinsa). A kokarin dagewa wajen sai an kare wata akida ya kai musulmi ga kirkirawa annabi karerayi tare da kawo rabe-raben kawuna a kan lamarin da bai shiga sharadin kasancewar mutum musulmi ba.
A ƙarshe mu san cewa kamar yadda Allah ya shardantawa annabawa ba su san wanene dan wuta ba, mu ma mabiya ya gargade mu cewa: Q2:134 “Waccan wata al’umma ce, ta riga ta shige, ta na da abinda ta sana’anta kuma kuma ku na da abinda kuka sana’anta. Kuma ba za’a tambaye ku ba daga abinda su ka kasance su na aikatawa.”
Amma akidar salafanci ta dage sai ta rabawa masu rai da marasa rai mazauni a wuta ko aljanna. Wannan kuwa hurumi ne na Allah shi kadai, ko annabawa bai basu shi ba. A yi hattara!
Malam Ali manazarci ne kuma mazaunin birnin Kano
