Manoma ba su san an raba takin tallafi a Gaya ba — Sarkin Noman Gaya

Spread the love

Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano

Sarkin Noman Gaya, Alhaji Bello Abubakar, ya bayyana cewa manoman da ke ƙaramar Hukumar Gaya ba su amfana da tallafin takin da gwamnatin jihar ta ce ta raba domin bunƙasa harkar noma ba.

Ya ce duk da cewa an bayyana cewa an kai takin tallafi har kimanin tireloli biyu zuwa Gaya, su a matsayinsu na wakilan manoma ba su san lokacin da aka raba takin ba.

“An raba taki har ya kai tireloli biyu a Gaya, amma mu ba mu san lokacin da aka raba shi ba,” in ji Sarkin Noman.

Alhaji Bello ya bayyana hakan ne lokacin da manema labarai suka kai masa ziyara a gidansa da ke garin Gaya, domin jin ta bakinsa dangane da ikirarin gwamnatin jihar na raba kayan tallafi domin bunƙasa aikin noma.

Ya ce yana da masaniyar cewa an raba wani kaso na takin a cikin ƙaramar hukumar, amma ya yi zargin cewa an raba shi ne ta hannun ’yan siyasa, ba tare da tuntubar shugabannin manoma ba.

A cewarsa, yana da Sarakunan Noma 17 a ƙarƙashinsa, amma ya ce babu ko guda daga cikinsu da aka bai wa tallafin.

Ya ƙara da cewa wasu daga cikin Sarakunan Noma a wasu ƙananan hukumomi sun shaida masa cewa shugabanninsu sun tuntube su lokacin rabon takin, amma a Gaya ba wanda ya tuntube shi ko wani daga cikin wakilan manoma.

Sarkin Noman ya yi kira ga gwamnati da ta ƙara tallafa wa manoma, musamman wajen rage tsadar kayan aikin noma kamar taki, magungunan kwari da ciyawa, tare da samar da ingantaccen iri.

Ya ce irin wannan tallafi zai taimaka wajen bunƙasa noma da samar da wadataccen abinci ga al’umma.

By ukarofi

Leave a Reply