Tsohon zakaran damben ajin masu nauyi na duniya, Tyson Fury, ya tabbatar da cewa an kusa cimma matsaya kan fafatawar da aka daɗe ana jira tsakaninsa da ɗan damben Birtaniya ɗan asalin Nijeriya, Anthony Joshua, inda aka tsara gudanar da damben a filin Madison Sƙuare Garden da ke birnin New York na Amurka.
Fury ne ya bayyana hakan a shafinsa na Instagram, inda ya wallafa hoton tallata damben da ke nuna shi da Joshua a gaban hoton gine-ginen birnin New York. Sai dai bai bayyana takamaiman ranar da za a yi damben ba.
Fury ya rubuta cewa, “Wane irin wuri ne NYC, wane irin filin wasa ne MSG, kuma wane irin faɗa ne Fury da AJ, a ƙasar da ake samun damar yin komai.”
Ya kuma ƙara da cewa:, “Wane irin ƙarshen mako ne za mu yi tare da abokai a New York. Abu ne na tarihi! Ba a daɗe ba, jama’a.”
Duk da wannan sanarwar ta Fury, Joshua da mai tallata wasanninsa, Matchroom Boxing, ba su tabbatar da cewa Madison Sƙuare Garden ne za a gudanar da damben ba a lokacin da rahoton ya fito. Batun zaɓen birnin New York ya kasance ɗaya daga cikin manyan batutuwan da ake tattaunawa a yayin shawarwarin shirya damben.
Rahotanni sun nuna cewa ana sa ran gudanar da damben a watan Nuwamba, inda ake duba ranar 20 ga watan a matsayin ranar da za a iya fafatawar.
Ana kuma shirin gudanar da damben ne a ƙarƙashin wata yarjejeniya da hamshakin attajirin Saudiyya kuma shugaban harkokin nishaɗi na ƙasar, Turki Alalshikh, ke mara wa baya, tare da haɗin gwiwar kamfanin watsa shirye-shiryen Netflix.
Da farko, Joshua ya fi son a gudanar da damben a Birtaniya, inda aka yi la’akari da filin Wembley Stadium a matsayin ɗaya daga cikin wuraren da suka dace.
Sai dai masu shirya damben sun karkata wajen gudanar da shi a Amurka, inda Madison Sƙuare Garden ya zama wurin da ya fi samun karɓuwa.
