Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Rundunar ’yan sandan Jihar Kano ta karɓi baƙuncin wata tawaga daga Kwamitin Zaman Lafiya na ƙasa (National Peace Committee), ta hannun Sakatariyar Cibiyar Kukah, domin ƙarfafa haɗin gwiwa da tattaunawa da masu ruwa da tsaki gabanin babban zaɓen shekarar 2027.
Tawagar ta ziyarci rundunar ne a ranar Talata, 1 ga Satumbar 2026, ƙarƙashin jagorancin Mista Espom Ajanya, ƙaramin Manajan Shirye-shirye na Cibiyar Kukah, wadda ke aiki a matsayin Sakatariyar Kwamitin Zaman Lafiya na ƙasa.
Da yake jawabi yayin ziyarar, Ajanya ya ce tattaunawar na daga cikin shirye-shiryen Kwamitin Zaman Lafiya na ƙasa gabanin babban zaɓen 2027.
Ya ce kwamitin, ta hannun sakatariyarsa, na tattaunawa da muhimman masu ruwa da tsaki a faɗin ƙasar domin nazarin yanayin zaɓe da tsaro, gano matsalolin da ka iya tasowa da kuma damar haɗin gwiwa wajen samar da zaɓe cikin zaman lafiya.
“Mun zo ne domin tattauna yanayin zaɓe da tsaro a Jihar Kano, da magance damuwar da ka iya tasowa, tare da binciko hanyoyin haɗin gwiwa da za su ƙarfafa zaman lafiya da kuma taimakawa wajen gudanar da zaɓen 2027 cikin lumana,” inji shi.
Tawagar ta yaba wa rundunar ’yan sandan Jihar Kano kan ƙwarewa, dabarun aikin ’yan sanda na rigakafi da kuma ƙoƙarin da take yi na tabbatar da zaman lafiya da tsaro a jihar.
Da yake mayar da martani, Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, PhD, ya maraba da tawagar tare da bayyana ziyarar a matsayin mai muhimmanci kuma ta zo a kan lokaci.
Ya jaddada muhimmancin tabbatar da zaman lafiya kafin, lokacin da kuma bayan gudanar da zaɓe.
“Zuwanku ya zo a daidai lokacin da ya dace. Abu na farko da muke buƙata shi ne zaman lafiya. Mun shirya tsaf domin zaɓen, kuma muna kira ga mutanen kirki na Jihar Kano da su guji duk wani abu da zai kawo cikas ga zaman lafiya yayin zaɓen da ke tafe,” inji CP Bakori.
Kwamishinan ’yan sandan ya tabbatar wa tawagar cewa rundunar a shirye take ta yi aiki tare da hukumomin da suka dace, ciki har da sauran hukumomin tsaro, Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC) da sauran masu ruwa da tsaki, domin tabbatar da samar da yanayi mai aminci da kwanciyar hankali wajen gudanar da babban zaɓen 2027.
Ya ce rundunar ta riga ta fara horas da jami’anta kan harkokin tsaron zaɓe, tare da tattaunawa da masu ruwa da tsaki a harkokin siyasa, gudanar da gagarumin wayar da kai ga jama’a da kuma ƙara ƙarfafa hanyoyin tattara bayanan sirri.
Rundunar ’yan sandan Jihar Kano ta yaba wa Kwamitin Zaman Lafiya na ƙasa bisa wannan tattaunawa, tare da sake jaddada aniyarta ta ci gaba da tattaunawa, haɗin gwiwa da kusantar al’umma domin tabbatar da zaman lafiya, tsaron jama’a da kare rayuka da dukiyoyi kafin, lokacin da kuma bayan babban zaɓen 2027.
