Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Rundunar ‘yan sanda a Katsina ta sanar da kama mutane 247 bisa aikata laifuka da suka haɗa da mutane 20 zargin aikata fyaɗe da luwaɗi a watan Agusta da ya gabata.
A hira da manema labarai a ofishin sa , jami’in hulɗa da jama’a na rundunar DSP Abubakar Sadiq Aliyu yace ‘yan sanda sun kuma kama ‘yan bindiga 31 da mutane huɗu da ake zargi masu ba ‘yan bindiga bayanan sirri, sai mutum uku da ake zargi da satar mutane.
DSP Abubakar Sadiq ya bayyana cewar sun sami nasarar ceto mutane 17 daga hannun ‘yan bindiga waɗanda bayan duba lafiyar su aka sada su da iyalan su.
Mutane 160 da ake zargi da aikata laifuka daban daban duk suna hannu, DSP Abubakar yace.
Haka kuma rundunar sun gabatar da waɗanda ake zargi 89 a gaban kotu da ɗaukar mataki akan laifuka daban daban.
‘Yan sanda sun kuɓutar da mutane 17 daga hannun ‘yan bindiga,waɗanda bayan duba lafiyar su aka sada su da iyalan su.
DSP Abubakar Sadiq ya baytana kayan da ‘yan sanda suka kama a hannun waɗanda ake zargi da suka haɗa da bindaga ƙirar AK-47 guda ɗaya da mota ɗaya.
Saura sun haɗa da babura 6, dabbobi 145 da keken ɗinki sai buhu uku na ‘yan ƙwamaso da katin waya da dama.
Akwai kwalbar tramadol guda 141 da kwayar extol 5 sai kwalbar Blue spirit da wayar layin wutar lantarki.
Yace duk waɗannan kayan da rundunar ta kama suna hannun su a matsayin shaidu da za su gabatar a kotu.
