Yadda masu tona kabari suka bayyana sirrin cire sassan jikin gawa don yin tsafin kuɗi

Spread the love

Wani abin al’ajabi ya fito fili bayan wasu mutane da ake zargi da tona kaburbura da cire sassan jikin mamata domin yin tsafin neman kuɗi sun bayyana yadda suka shiga wannan mummunar sana’a, da kuma irin abubuwan da suke cirewa daga jikin gawawwaki.

Wasu daga cikin mutane 10 da Rundunar ’Yan Sandan Jihar Oyo ta kama bisa zargin safarar sassan jikin ɗan adam domin yin tsafin neman kuɗi sun bayyana wa ’yan jarida yadda suke gudanar da wannan aiki.

Mutanen sun bayyana cewa suna zuwa maƙabartar Musulmi da ke garuruwan Iseyin da Saki, inda suke tono sababbin kaburbura bayan an binne mamata, sannan su cire wasu sassan jikin gawawwakin domin sayarwa ga masu amfani da su wajen tsafi.

A yayin gabatar da waɗanda ake zargin ga ’yan jarida a Ibadan, Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Oyo, DSP Ayanlade Olayinka, ya ce binciken farko ya nuna cewa mutanen suna da hannu wajen tona kaburbura da safarar sassan jikin mamata.

Sai dai abin da ya fi ɗaukar hankali shi ne yadda wasu daga cikin waɗanda ake zargin suka bayyana cewa wani mutum da suke kira “Dakta”, wanda ke gudanar da wani ƙaramin asibiti a Saki kafin rasuwarsa, shi ne ya koya musu yadda ake tona kabari da cire sassan jikin gawa.

ɗaya daga cikin waɗanda ake zargin, manomi mai suna Alfa Taofeek Rahman, mai shekara 46, ya ce wani “Dakta” ne ya fara shigar da shi cikin wannan aiki.

Ya ce, kafin mutumin ya rasu, yana ɗaukar hayar babur zin da yake tuƙa shi cikin dare zuwa maƙabarta, inda yake jira a wani wuri yayin da “Dakta” ke gudanar da aikin tono kabari.

“Dakta ne ya sa ni cikin wannan sana’a. Kafin ya rasu, yana ɗaukar hayar babur da nake goya shi cikin dare zuwa maƙabarta, inda nake ɓoyewa a wani wuri yayin da yake aikin haƙar kabari.

“Yana biya na idan ya sayar da abin da ya cire daga jikin gawa,” inji shi.

Rahman ya ce, sukan tafi ne da tsakar dare zuwa wata maƙabartar Musulmi da ke kan hanyar Saki zuwa Ago-Are, inda suke gudanar da aikin kafin gari ya waye.

Bayan rasuwar mutumin, ya ce ya ci gaba da gudanar da aikin shi kaɗai.

Ya bayyana cewa, daga cikin sassan jikin da suka fi cirewa akwai zuciya, tsokar nama da zira’in hannu, inda suke amfani da wasu sunaye na ɓoye wajen kiransu.

A cewarsa, suna kiran zuciya da “Tumatir”, tsokar nama da “Burodi”, yayin da zira’in hannu suke kira “fankar hannu” ko “abebe”.

Wani da ake zargin, Adam Ibrahim, mai shekara 42, ya ce shi ɗan ƙasar Togo ne kuma ya shafe shekaru tara yana aikin leburanci a Saki.

Ya ce ya auri ’yar Nijeriya kuma suna da ɗa guda.

Ibrahim ya ce, kimanin shekaru biyar da suka gabata ne “Dakta” ya gayyace shi domin ya shiga aikin tona kaburbura.

“Ban san irin wannan aiki a Togo ba sai da na zo Najeriya, inda Dakta yake ba ni Naira dubu 20 a duk lokacin da ya tono gawa a maƙabarta,” inji shi.

Shi kuwa Jimoh Muritala, mai shekara 35, ya ce Taofeek ne ya koya masa aikin tonon kabari.

Ya ce sukan yi aikin tare, kuma Taofeek yana ba shi Naira dubu 20 a matsayin ladan aikin.

“Talauci ne ya jefa ni cikin wannan sana’a, domin ina zaune da iyali a garin Saki ba tare da aikin komai ba,” inji shi.

Wani da ake zargin mai suna Abiola Nasiru, mai shekara 45, wanda ya ce shi malamin tsubbu ne, ya bayyana cewa yana kiran “Dakta” domin ya samo masa sassan jikin mutum da yake buƙata wajen haɗa magungunan tsafi.

Ya ce, ana amfani da wasu daga cikin sassan jikin wajen haɗa wani sabulu da ake ikirarin yana taimakawa wajen samun arziki cikin dare ɗaya.

“Ina kiran Dakta ya kawo min irin sassan jikin mutum da nake buƙata domin haɗa maganin samun arziki cikin dare ɗaya.

“Akwai sabulun da nake haɗawa da sassan jikin mutum tare da wasu magunguna. Muna kwaɓawa ne sannan mu sayar wa mabuƙata waɗanda suke yin wanka da shi.

“Mabuƙatan suna sayen sabulun tsafin a kan Naira dubu 100 zuwa sama, ba tare da sun san cewa an haza sassan jikin mutum a cikinsa ba,” inji shi.

Nasiru ya ƙara da cewa wasu daga cikin mutanen da suke sayen magungunan sun daina komawa wurinsa bayan sun kasa samun abin da suke fata.

Tijani Wasiu, mai shekara 54, ya ce ya taɓa neman taimakon wani mutum mai suna Suleiman domin ya sayo masa sassan jikin mutum daga wurin “Dakta”.

Ya ce ya yi amfani da sassan wajen wani abu da yake fata zai taimaka masa, amma bai samu nasarar da yake nema ba.

“Na aika Suleiman ya sayo min sassan jikin mutum daga wurin Dakta, wanda na yi amfani da shi ba tare da samun nasara ba. Ina shirin sake aikawa ne aka kama mu,” inji shi.

Wani mutum mai suna Busari Sulaiman, mai shekara 47, wanda ya bayyana kansa a matsayin malamin makarantar allo, ya ce an kama shi ne saboda ya taimaka wa wani abokinsa wajen sayen sassan jikin mutum.

Ya ce ya sayi sassan ne kan Naira dubu 5 daga hannun Taofeek, kuma ya taɓa yin hakan sau biyu.

“An kama ni ne saboda na taimaka wa abokina sayen sassan jikin mutum a kan Naira dubu 5 daga hannun Taofeek. Sau biyu ina sayo wa abokina irin abin da yake so. Ni dai ban ci moriyar wannan sana’a ba,” inji shi.

Lokacin da aka tambayi waɗanda ake zargin dalilin da ya sa ba su yi amfani da irin wannan tsafin domin neman kuɗi ga kansu ba, dukkansu sun bayar da amsa iri ɗaya.

Sun ce ba ƙaddara ce su samu dukiyar ta wannan hanya ba.

“Ko mun yi amfani da sabulun tsafin, ba zai yi aiki a kanmu ba,” inji su.

A halin yanzu, Rundunar ’Yan Sandan Jihar Oyo na tsare da mutanen, yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike a Sashen Binciken Manyan Laifuka (SCID) da ke Iyaganku, Ibadan.

Kakakin rundunar ya ce za a gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu da zarar an kammala binciken.

By ukarofi