
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A ranar Talata ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi ya fuskanci tsaiko yayin da ya yi ƙoƙarin shiga yankin Yelwata a Jihar Benuwai bayan wasu matasa sun yi cincirindo kan hanyar Gboko a Makurɗi, babban birnin jihar, lamarin da ya haddasa cinkoson ababen hawa da tilasta wa tawagar tsohon gwamnan Jihar Anambaran ja da baya.
Masu zanga-zangar, waɗanda suke rera “We don’t want Peter Obi”, sun tare hanyar ne a kusa da Sansanin Sojojin Saman Nijeriya da filin jiragen sama na Makurɗi na tsawon sa’o’i yayin da Peter Obi ya nufi zuwa Yelwata domin jajenta wa iyalan mutanen da aka yi wa kisan gilla a watan Yunin 2025.
Rahotanni sun ce, al’amarin ya janyo rikici tsakanin ‘yan tawagar Obi, gwamnatin Jihar Benuwai da ‘yan sanda kan ko an yi sanarwar da ta dace akan ziyarar da kuma waye ne ke da alhakin tare hanyar.
Da yake tsokaci a wajen a wani bidiyo da aka yaɗa ta gidan talabijin na News Central daga shafin X a ranar Talata, Obi ya ce ya yi tafiya zuwa Benuwai ne da nufin jajenta wa mutanen da kashe-kashe ya shafe su, amma an dakatar da su bisa umarnin wani maitaimakin gwamnati (SA). “An faɗa min cewa matasa, ƙarƙashin jagorancin wani SA ga gwamnatin, sun yanke shawarar tare hanyar kuma sun tabbatar ban samu zuwa wajen ba,” inji shi.
Ya bayyana hakan a matsayin abin da ba za su lamunta ba kuma ya zargi waɗanda suke da hannu a ciki da amfani da yunwa da matasan da aka bari kara zube wajen cimma manufar siyasa.
Saidai, gwamnatin Benuwai a nata ɓangaren, ta nesanta kanta da hannu a faruwar wannan al’amari, tana mai cewa ba ta ma san cewa Obi zai kai ziyara jiharta ba. Sakataren yaɗa labarai ga Gwamna Hycinth Alia na jihar, Kula Tersoo ne ya faɗi haka a wata hira ta wayar tarho a ranar Talata, inda ya gwamnatin ba ta masaniyar zuwan Obo, yana mai iƙirarin cewa ɗan takarar shugaban ƙasar bai je da wadatattun jami’an tsaro ba.
Ya kuma bayyana cewa ya yi mamakin cewa matasa za su iya dakatar da Obi shiga jihar, yana mai cewa babu wani matashi da yake aiki a madadin gwamnatin, sannan Obi ba barazana ba ne ga gwamnan jihar.
A wani ɓangare kuwa, ɗan takarar gwamnan Benuwai a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar NDC, Farfesa Terhemba Shija, ya ce tawagar Obi ta sanar da hukumomin tsaro a jihar batun ziyarar.
Al’amarin ya auku ne a lokacin da Obi da ‘yan tawagarsa ke ƙoƙarin tafiya garin Yelwata, kuma tuni ya koma Abuja, kamar yadda wakilinmu ya samu labari yayin haɗa wannan rahoto.
