Matashin Kano ya yanke yatsarsa kan alƙawarin miliyan N80 na tsafi

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMAMD

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta kama wasu mutane biyar, ciki har da wani matashi mai shekaru 27 da ake zargi da yanke yatsarsa da kansa bayan an yi masa alƙawarin ba shi Naira miliyan 80 a wani lamari da ake zargin yana da alaƙa da tsafi.

Mai magana da yawun Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar 29 ga Agusta 2026, bayan matashin mai suna Yusuf Mahmuda, ɗan asalin Rano, ya je ofishin ’yan sanda domin kai ƙorafi.

A cewar Kiyawa, Yusuf ya shaida wa ’yan sandan cewa wani mutum ya nemi ya samo masa yatsar ɗan Adam mai rai, inda ya yi masa alƙawarin biyan sa Naira miliyan 80 idan ya kawo ta.

Sai dai bayan ya kasa samun wanda zai ba shi yatsar, Yusuf ya ɗauki wuƙa ya yanke yatsarsa ta hannun hagu da kansa, sannan ya miƙa ta ga mutumin da ya yi masa wannan buƙata.

Daga bisani, matashin ya garzaya wajen ’yan sanda domin kai ƙorafi, yana mai cewa mutumin bai cika alƙawarin da ya yi masa na biyan Naira miliyan 80 ba.

Kiyawa ya ce, binciken da ’yan sanda suka gudanar bayan karɓar ƙorafin ya kai ga cafke wasu mutane huɗu da ake zargi da hannu a lamarin, tare da Yusuf.

Waɗanda aka kama sun haɗa da Abdurrahman Abbas, mai shekaru 45, mazaunin Kwassangami a ƙaramar Hukumar Gezawa; Abubakar Iliyasu, mai shekaru 35, daga Zangon Dakata a cikin birnin Kano; Shu’aibu Awale, mai shekaru 55, daga Daganawa a ƙaramar Hukumar Bunkure; da Ishaka Isa, mai shekaru 26, ɗan Rano.

Kakakin ’yan sandan ya ce, jami’an tsaro sun kuma gano yatsar da aka yanke, da kuma wuƙar da aka yi amfani da ita wajen aikata abin.

Ya ƙara da cewa, ’yan sandan sun kuma cafke mutumin da ake zargi da kasancewa wanda ya shirya wannan al’amari.

Kiyawa ya bayyana cewa a ranar Laraba ne aka gurfanar da dukkan mutanen biyar a gaban Kotun Shari’a da ke Jogana, a ƙaramar Hukumar Gezawa, inda ake tuhumar su da laifin haɗa baki wajen aikata laifi da kuma yunƙurin aikata tsafi.

By ukarofi