Tsadar lantarki ya jefa masana’antun Nijeriya cikin mawuyacin hali — MAN

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Masana’antun Nijeriya sun kashe zunzurutun kuɗi har Naira tiriliyan 1.34 wajen samar da wutar lantarki ta wasu hanyoyi a shekarar 2025, yayin da yawan katsewar wutar lantarki ya tilasta musu dogaro da janareto masu amfani da dizal, gas, LPFO da sauran hanyoyin samar da wuta daga wajen babban layin lantarkin ƙasa.

Bayanan da ƙungiyar Masana’antun Nijeriya (MAN) ta tattara na musamman sun nuna cewa kuɗin da masana’antun suka kashe wajen samar da wutar madadin ya ƙaru da kusan kashi 21 cikin 100, daga Naira tiriliyan 1.11 a shekarar 2024 zuwa Naira tiriliyan 1.34 a 2025.

Wannan na ƙara bayyana irin nauyin da rashin ingantacciyar wutar lantarki ke ɗora wa masana’antun ƙasar, musamman yayin da ake samun raguwar amincin babban tsarin samar da wutar lantarki na ƙasa.

Bayanan MAN sun nuna cewa matsalar ta ƙara tsananta a shekarar 2025, inda matsakaicin lokacin da ake samun wutar lantarki a kullum ya ragu daga sa’o’i 16.7 a farkon rabin shekarar zuwa sa’o’i 13.1 a rabin shekarar na biyu.

Hakan na nufin masana’antun na ƙara ɗaukar nauyin samar da wani babban kaso na wutar da suke buƙata da kansu domin kada ayyukan masana’antunsu su tsaya.

Bayanan MAN sun kuma nuna cewa kuɗin da masana’antun ke kashewa wajen samar da wutar madadin ya yi ta ƙaruwa sosai cikin shekaru goma da suka gabata, duk da cewa an samu raguwa a wasu shekarun.

A shekarar 2014, masana’antun sun kashe Naira biliyan 25 wajen samar da wutar madadin. Adadin ya tashi zuwa Naira biliyan 59 a 2015, sannan ya kai Naira biliyan 129.95 a 2016.

A shekarar 2017, kashe-kashen sun ragu zuwa Naira biliyan 117.4, sannan suka ƙara raguwa zuwa Naira biliyan 93.11 a 2018 da Naira biliyan 61.38 a 2019.

A shekarar 2020, adadin ya sake tashi zuwa Naira biliyan 81.91 kafin ya ragu zuwa Naira biliyan 71.22 a 2021.

Sai dai daga shekarar 2022 aka fara samun gagarumin tashin farashin samar da wutar madadin, inda masana’antun suka kashe Naira biliyan 144.5 a wannan shekarar.

A shekarar 2023 kuma, adadin ya yi tashin gwauron zabi zuwa Naira biliyan 781.7, kafin ya ƙetare alamar tiriliyan ɗaya a 2024, lokacin da ya kai Naira tiriliyan 1.11.

Zuwa shekarar 2025, kuɗin samar da wutar madadin ya ƙara hawa zuwa Naira tiriliyan 1.34, wanda ke wakiltar ƙarin kashi 71.4 cikin 100 idan aka kwatanta da Naira biliyan 781.68 da aka kashe a 2023.

Wannan yanayi ya jawo damuwa kan yadda masana’antun Nijeriya za su iya yin gogayya da na sauran ƙasashe, musamman ganin yadda ƙarfin sayen kayayyaki na ’yan ƙasa ke ci gaba da yin rauni, yayin da kuɗaɗen gudanar da kamfanoni ke ƙara matsa musu lamba.

Masu ruwa da tsaki a masana’antun sun jaddada buƙatar samar da wutar lantarki mai inganci daga babban layin ƙasa, tare da ƙara zuba jari a wasu hanyoyin samar da makamashi, domin rage dogaro da janareton dizal mai tsada.

MAN, ƙarƙashin jagorancin Segun Ajayi-Kadir, ta ce: “Amincin wutar lantarki daga babban layi ya tabarbare sosai, inda yawan lokacin samun wuta a kullum ya ragu daga sa’o’i 16.7 a rabin farko na 2025 zuwa sa’o’i 13.1 a rabin na biyu.”

Binciken da wannan jarida ta gudanar ya nuna cewa masana’antun da dama ba sa ƙara dogaro da Kamfanonin Rarraba Wutar Lantarki (DisCos) wajen samar da wutar da suke amfani da ita a masana’antunsu, inda suke amfani da gas ko LPFO a kai a kai domin kauce wa asarar da katsewar wuta ke haddasawa a lokacin samar da kayayyaki.

Daga cikin kamfanonin da aka ce sun koma samar da wutar kansu a masana’antunsu akwai Flour Mills of Nigeria, Dangote Group, Cadbury, Haffar, Kam Industries, Nigerian Breweries Plc, Lafarge Africa, Procter and Gamble Nigeria Limited, Bankin Masana’antu (Bank of Industry), Seven-Up Bottling Company Plc, Dangote Cement Plc, Lekki Port LFTZ Enterprise Limited, Guinness Nigeria Plc, Nestle Nigeria Plc da Aluminium Smelter Company of Nigeria.

Sauran sun haɗa da De-United Foods Industries Limited, Sagamu Steel Nigeria Limited, British American Tobacco Nigeria Limited, Unilever Nigeria Plc, Total E & P Nigeria Limited da Mikano International Limited, a cewar Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Nijeriya (NERC).

A shekarar 2025, Hukumar NERC ta bai wa Pure Flour Mills Limited, wani kamfanin masana’antu da ke Jihar Ribas, lasisin samar da wutar lantarki mai ƙarfin megawatt 546.

Shi ma Dangote Industries Limited ya samar da kusan megawatt 1,500 na wutar lantarki a shekarar 2025, a cewar shugaban kamfanin, Aliko Dangote.

Matatar Dangote ita kaɗai na da tashar samar da wutar lantarki mai ƙarfin megawatt 435 a shekarar 2025, ƙarfin da aka ce ya isa ya biya dukkan buƙatar wutar lantarki ta Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Ibadan.

A cewar NERC, United Cement Company of Nigeria Limited na samar da megawatt 105, Flour Mills of Nigeria Plc na samar da megawatt 70, yayin da Lafarge Cement Wapco Nigeria Plc ke samar da megawatt 90.

By ukarofi

Leave a Reply