Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe
Ɗan takarar gwamnan Jihar Gombe na jam’iyyar APC, Alhaji Dakta Jamilu Isyaku Gwamna, ya yi watsi da wani faifan bidiyo da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta, wanda ake amfani da shi wajen nuna cewa har yanzu yana goyon bayan tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar.
Gwamna ya bayyana cewa bidiyon tsoho ne, kuma an ɗauke shi ne a lokacin da yake ɗaya daga cikin jiga-jigan jam’iyyar PDP, kafin daga bisani ya sauya sheƙa zuwa APC tare da mara wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya a zaɓen shugaban ƙasa na 2023.
A cewarsa, kalaman da suka fito a cikin bidiyon sun yi daidai da matsayin siyasar da yake da shi a lokacin, domin a wancan lokaci yana cikin PDP ne kuma jam’iyyar ta tsayar da Atiku a matsayin ɗan takararta na shugaban ƙasa.
“Na ga bidiyon kuma na san shi. Amma an ɗauke shi ne a lokacin da nake cikin PDP, kafin Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya fito takara.
“A lokacin muna PDP kuma muna goyon bayan Atiku Abubakar. Amma bayan na koma APC, na zama kodinetan yaƙin neman zaɓen Tinubu-Shettima a 2023. Mun goyi bayan Tinubu muka bar Atiku,” in ji shi.
Ɗan takarar ya ce sake fitar da bidiyon a wannan lokaci ba tare da bayyana lokacin da aka ɗauke shi ba, na iya yaudarar jama’a tare da ƙirƙirar fahimtar da ba ta dace da matsayinsa na siyasa a yanzu ba.
Ya zargi wasu da amfani da tsofaffin bayanai da bidiyoyi domin cimma wasu manufofin siyasa, musamman a daidai lokacin da zaɓe ke ƙara matsowa.
“Kafofin sada zumunta wuri ne da ake iya ɗauko tsohon abu a sake yaɗa shi domin cimma wata manufa.
“An fitar da wannan bidiyo yanzu ba tare da muhallin lokacin da aka ɗauke shi ba. An yi hakan ne domin wata manufar siyasa. Don haka ina kira ga magoya bayanmu da al’ummar Gombe da su yi watsi da shi,” ya ƙara da cewa.
Gwamna ya kuma yi kira ga magoya bayansa, mambobin APC da masu goyon bayan Shugaba Tinubu da kada su bari bidiyon ya ɗauke musu hankali ko ya haifar da rikici a tsakaninsu.
Ya buƙace su da su kasance masu natsuwa tare da guje wa duk wani abu da ka iya haifar da tashin hankali ko saɓani yayin da harkokin siyasa ke ƙara ɗaukar zafi a jihar.
A cewarsa, ya kamata a fi mayar da hankali kan matsayi, manufofi da ayyukan ’yan siyasa na yanzu, maimakon amfani da tsofaffin kalamai ko bidiyoyi da aka cire daga mahallinsu wajen tantance matsayinsu na siyasa.
