DSS za ta sake gurfanar da mutane biyar da ake zargi da ’yan Ansaru ne

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Hukumar Tsaro ta ƙasa (DSS) za ta sake gurfanar da wasu mutane biyar da ake zargi da kasancewa mambobin ƙungiyar ’yan ta’adda ta Ansaru, bisa zargin hannu a sace ɗalibai da malamai a ƙaramar hukumar Oriire ta Jihar Oyo a ranar 15 ga Mayu, tare da kashe biyu daga cikin waɗanda aka sace.

Blueprint Manhaja ta ruwaito cewa za a sake gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja a ranar Alhamis, bisa sabon tuhume-tuhume mai ƙunshi laifuka shida, mai lamba FHC/ABJ/CR/438/2026.

Daraktan Masu Gabatar da ƙara na Tarayya (DPPF), Rotimi Oyedepo, SAN, ne ya shigar da tuhume-tuhumen a madadin Gwamnatin Tarayya.

Waɗanda ake tuhumar sun haɗa da Mahmud Muhammad, wanda aka fi sani da Abu Bara’a da Abbas Mukhtar; Abubakar Abbas, wanda aka fi sani da Isah Adam da Mallam Mahmuda Al-Nigeri; Abdulrazak Umar, wanda aka fi sani da Abu Khalifa da Abu Khalid; Yunusa Musa, wanda aka fi sani da Abu Yunusa Bin Musa; da Shamsu Adamu Sani, wanda aka fi sani da Abu Itisar.

An shirya gurfanar da mutanen ne a ranar Laraba, amma aka dakatar da shari’ar bayan wanda ake tuhuma na farko, Muhammad, ya nuna rashin amincewarsa da a wakilci shi da wani lauya daga Hukumar Kula da Taimakon Shari’a (Legal Aid Council).

Mataimakin Darakta na Legal Aid Council, Akilaluyel Shettima, ne ya bayyana cewa shi ne zai wakilci dukkan mutanen biyar yayin da shari’ar ta zo gaban Mai Shari’a Salim Ibrahim.

Sai dai Muhammad, wanda ya yi magana a madadin sauran waɗanda ake tuhuma, ya shaida wa kotun cewa a baya wani lauya mai suna Bala Dakum ne yake wakiltarsu, kuma suna son ya ci gaba da kare su.

“Mun kasance muna samun wakilcin Bala Dakum a matsayin lauyanmu a baya, kuma muna son ya ci gaba da kare mu,” inji shi.

Da yake mayar da martani, DPPF Rotimi Oyedepo, SAN, ya amince cewa haƙƙin wanda ake tuhuma na samun lauya da ya zaɓa wani batu ne da kundin tsarin mulki ya tanada kuma ya kamata a mutunta shi.

Oyedepo ya kuma shaida wa kotun cewa DSS hukuma ce mai bin doka, kuma ba ta da niyyar tsananta wa waɗanda ake tuhuma, sai dai tabbatar da cewa an yi adalci.

Bayan haka, Mai Shari’a Saliu Ibrahim ya ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar Alhamis domin sake gurfanar da waɗanda ake tuhuma.

Alƙalin ya umarci mutanen da ake tuhuma da su tuntubi lauyansu, Bala Dakum, tare da tabbatar da cewa ya halarci zaman kotun domin ci gaba da shari’ar.

Justice Ibrahim ya kuma umarci DSS da ta bai wa waɗanda ake tuhuma damar ganawa da lauyansu domin su samu damar shirya kariyarsu yadda doka ta tanada.

By ukarofi

Leave a Reply