Majalisar Tarayyya ta aika ƙudirin gyaran kundin tsarin mulki zuwa majalisun jihohi 36

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Majalisar Tarayyar Nijeriya ta tura ƙudirin Gyaran Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Nijeriya na 1999, wanda aka fi sani da “Sixth Alteration Bill, 2026”, zuwa majalisun dokokin jihohi 36 domin duba shi da kuma amincewa da shi, a matsayin wani muhimmin mataki na ci gaba da aikin sake duba Kundin Tsarin Mulkin ƙasar.

Blueprint Manhaja ta ruwaito cewa, Magatakardar Majalisar ƙasa, Kamoru Ogunlana, ne ya aika da kudirin a hukumance ranar Laraba, 16 ga Satumba, 2026, bisa umarnin shugabannin Majalisar ƙasa, tare da bin tanadin Sashe na 9 na Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya na 1999, kamar yadda aka yi masa gyara.

Matakin ya kuma yi daidai da tanadin Sashe na 9 na Kundin Tsarin Mulkin, wanda ya bayyana cewa duk wani kudirin sauya kundin tsarin mulki da Majalisar ƙasa ta amince da shi, sai ya samu goyon bayan akalla kashi biyu bisa uku na majalisun dokokin jihohi 36, wato majalisu 24 daga cikin 36, kafin a miƙa shi ga shugaban ƙasa domin amincewa da shi.

Ko da yake Kundin Tsarin Mulkin bai sanya wa majalisun dokokin jihohi wani wa’adin doka na musamman na mayar da sakamakon ƙuri’unsu ba, shugabancin Majalisar ƙasa ya tsara wa’adin gudanarwa na kwanaki 30 domin tabbatar da cewa an kammala aikin sauye-sauyen cikin tsari da kuma cikin lokaci.

A cikin wata sanarwa da Magatakardar Majalisar ƙasar ya fitar kan matakin, ya bayyana irin rawar da majalisun jihohi za su taka da kuma tsarin da zai jagoranci mataki na gaba na aikin.

Sanarwar ta ce: “Majalisar ƙasa ta fahimci nauyin da Kundin Tsarin Mulki ya ɗora wa Majalisun Dokokin Jihohi, kuma tana mutunta ’yancinsu wajen duba Kudirin. Aika kudirin na da nufin ba su damar gudanar da wannan nauyi na kundin tsarin mulki cikin tsari.”

Sanarwar ta ƙara da cewa: “Majalisar ƙasa ta ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da cewa ana gudanar da aikin sauya Kundin Tsarin Mulki ne bisa cikakken bin tanadin Kundin Tsarin Mulki, da kuma ka’idojin bin tsarin da ya dace, haɗin gwiwar hukumomi da kuma mutunta nauyin majalisa da aka ɗora wa kowane mataki na majalisa.”

Sanarwar ta kuma bayyana cewa, da zarar Majalisar ƙasa ta karɓi ƙudurin majalisun dokokin jihohi, za ta ɗauki matakan da suka dace bisa tanadin Kundin Tsarin Mulkin ƙasar.

Aika kudirin zuwa majalisun jihohi ya zo ne bayan wasu manyan yunƙurin dokoki da aka gudanar a majalisun dokokin biyu na Majalisar ƙasa cikin watannin baya, da nufin sauya wasu muhimman fannoni na tsarin tafiyar da mulkin Nijeriya.

Daga cikin muhimman kudurorin da ke cikin wannan zagayen gyaran Kundin Tsarin Mulkin akwai Kudirin Gyaran Kundin Tsarin Mulki kan ƙirƙirar ’Yan Sandan Jihohi na 2026.

Kudirin dai na neman kafa tsarin da zai bai wa jihohi damar samun tsarin ’yan sanda na kansu, domin kusantar da harkokin tsaro ga al’ummomin da ake gudanar da mulki a cikinsu. Kudirin ya samu kulawa sosai musamman bayan goyon bayan da shugaban ƙasa ya nuna masa, da kuma kafa wata ƙungiyar aiki da aka ɗora wa alhakin duba yadda za a samar da tsarin tsaro mai matakai biyu a Nijeriya.

Femi Gbajabiamila, wanda shi ne Shugaban ƙungiyar Aikin Shugaban ƙasa kan Kudirin Dokar ƙasa kan ’Yan Sanda, kuma Babban Hafsan Ma’aikatan Fadar Shugaban ƙasa, ya ce gyaran na da nufin kusantar da aikin ’yan sanda ga al’ummar Nijeriya tare da samar da matakan kariya da za su taimaka wajen ganin tsarin ya zama mai inganci kuma jama’a su amince da shi.

Gbajabiamila ya ce babban abin tambaya a yanzu ba wai kawai ko ya kamata a kusantar da aikin ’yan sanda ga jama’a ba ne, illa yadda za a cimma hakan ba tare da maye gurbin matsalolin da ake fuskanta a yanzu da wasu sababbi ba.

Ya kuma ce gyaran zai bai wa gwamnatocin jihohi ƙarin nauyin da ya kamata su ɗauka wajen tabbatar da tsaron al’ummomin da suke jagoranta, tare da tabbatar da cewa kusantar da harkokin tsaro ga al’umma ba zai kasance a kan hanyar tauye adalci ko haƙƙin ‘yan ƙasa ba.

By ukarofi

Leave a Reply