Ba a kawar da wariyar launin fata a Afirka ta Kudu ba sai da taimakon Nijeriya – Obasanjo

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Tsohon Shugaban Nijeriya, Olusegun Obasanjo, ya ce da ba don goyon bayan da Nijeriya ta bai wa gwagwarmayar yaki da mulkin wariyar launin fata ba, da Afirka ta Kudu ba ta kawo karshen mulkin wariyar launin fata a shekarar 1994 ba.

Obasanjo ya bayyana hakan ne a wata hira da shirin C-Suite Cafe, inda ya ce Nijeriya ta shiga gwagwarmayar ne saboda imanin cewa babu wani bakar fata da ya kamata a dauke shi a matsayin dan kasa ko mutum marar daraja saboda launin fatarsa.

Ya ce Nijeriya ta yi aiki tare da wasu shugabannin Afirka da na duniya wajen yaki da wariyar launin fata, ciki har da Julius Nyerere na Tanzania, Kenneth Kaunda na Zambia da Samora Machel na Mozambiƙue.

Obasanjo ya kuma yi Alla wadai da hare-haren kyamar bakin haure da ake kai wa ‘yan Afirka a Afirka ta Kudu, musamman ‘yan Nijeriya.

Ya ce ko da wasu bakin haure na iya kasancewa cikin kasar ba bisa ka’ida ba ko kuma sun aikata laifi, hakan bai ba da damar kai musu hari ko lalata gidaje da wuraren kasuwancinsu ba.

A makon da ya gabata ne Majalisar Dokokin Nijeriya ta dakatar da duk wata alaka ta ayyukan majalisa da Afirka ta Kudu saboda ci gaba da kai wa ‘yan Nijeriya hare-haren kyamar baki a kasar.

Rahotanni sun ce kusan ‘yan Nijeriya 100 ne aka kashe a hare-haren tsageru da na kyamar baki a Afirka ta Kudu tun daga shekarar 2022.

By ukarofi

Leave a Reply