Jirage 7,961 suka yi jigila a Agusta amma 4,765 sun samu jinkirin tashi – NCAA

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Kamfanonin jiragen sama na Air Peace da United Nigeria Airlines ne suka fi samun yawan jiragen da suka makara a tsakanin kamfanonin zirga-zirgar jiragen sama na cikin gida a Nijeriya a watan Agustan 2026.

Hakan na munshe ne cikin rahoton Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Nijeriya (NCAA), kan yadda zirga-zirgar jiragen saman cikin gida suka gudana a watan Agusta.

Bisa ga bayanan hukumar, Air Peace ta yi zirga-zirgar jirage 1,864 a cikin watan, inda 1,330 daga cikinsu suka samu jinkiri.

United Nigeria Airlines ce ta biyo bayanta, inda daga cikin jirage 1,231 da ta gudanar, 943 suka samu jinkiri. Enugu Air kuwa ta gudanar da jirage 878, inda 582 suka makara, yayin da Value Jet ta yi zirga-zirgar jirage 767, daga cikinsu 435 suka samu jinkiri.

Aero ta samu jinkirin jirage 246 cikin 469 da ta gudanar, yayin da Ibom Air ta samu jinkirin jirage 254 cikin 560. Arik Air kuma ta samu jinkirin jirage 188 daga cikin 301 da ta gudanar.

Haka kuma, Maɗ Air ta samu jinkirin jirage 204 cikin 336, yayin da Rano Air ta samu jinkiri a jirage 216 cikin 503 da ta gudanar.

Overland ta samu jinkirin jirage 139 cikin 239, yayin da Green Africa ta samu jinkirin jirage 114 cikin 226. Binani ta samu jinkirin jirage 22 cikin 57, yayin da ɗe Jet ta samu jinkiri a jirage 40 cikin 127. Umza Air ta samu jinkirin jirage 52 cikin 403 da ta gudanar. Ita kuwa NGEAGLE ba ta gudanar da wani jirgin sama ba a tsawon lokacin.

A dunƙule, kamfanonin jiragen saman sun gudanar da zirga-zirgar cikin gida guda 7,961 a watan Agusta, inda 4,765 daga cikinsu suka samu jinkiri.

Daga cikin jiragen da suka samu jinkirin, 2,801 sun makara tsakanin mintuna 16 zuwa awa guda, yayin da 1,322 suka samu jinkirin da ya kai tsakanin awa daya zuwa biyu.

Hukumar ta ce, wasu jirage 407 sun samu jinkirin da ya kai tsakanin sa’o’i biyu zuwa uku, yayin da wasu 235 suka makara na tsawon sa’o’i uku ko fiye.

Baya ga jinkirin, kamfanonin jiragen saman sun soke zirga-zirgar jirage 36 a cikin watan Agusta. United Nigeria ce ta fi yawan soke jirage, inda ta soke guda takwas, sai Air Peace da ta soke guda bakwai, sannan Enugu Air da ta soke guda huɗu.

A ranar 10 ga Satumba, Darakta-Janar na Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Nijeriya (NCAA), Chris Najomo, ya gargaɗi kamfanonin jiragen sama da su dauki matakan gaggawa kan yawaitar jinkirin jirage, ƙarancin ma’aikatan jirgi da sauran matsalolin da suka shafi haƙƙin fasinjoji.

Najomo ya buƙaci kamfanonin su tsara jadawalin zirga-zirgarsu bisa yawan jiragen da suke da su da kuma ma’aikatan jirgin da ke hannunsu, domin kauce wa yawan jinkiri da soke zirga-zirga. Ya kuma nuna shakku kan ingancin tsarin tanadin lokaci da kamfanonin ke amfani da shi, duba da yadda ake ci gaba da samun jinkiri da soke jirage.

Sai dai ya amince cewa wasu dalilai, ciki har da sauyin yanayi, karkatar da jirage zuwa wasu filayen sauka da tashi da kuma takunkumin da ake samu a filayen jiragen sama, na iya haifar da irin waɗannan matsaloli.

Darakta-Janar ɗin ya jaddada muhimmancin shirya matakan da za a ɗauka idan aka samu matsala, tare da samar da ingantaccen tsarin sanar da fasinjoji duk wani sauyi da ya shafi zirga-zirgarsu.

By ukarofi

Leave a Reply