Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Shugabannin Arewa da masu ruwa da tsaki a yankin sun amince cewa akwai matsalolin zamantakewa, siyasa da shugabanci da suka daɗe suna addabar yankin, suna mai gargaɗin cewa rashin tsaro, sakaci da ilimi, cin hanci da rashawa, rikicin ’yan siyasa da matsalar almajirai na barazana ga makomar Arewacin Nijeriya.
An bayyana hakan ne a cikin wata sanarwar matsaya da aka fitar bayan taron tunawa da marigayi Janar Hassan Usman Katsina karo na uku, wanda ƙungiyar New Vision Development Initiative (NEVDI) ta shirya a Gidan Arewa da ke Kaduna.
Kanal Lawan Gwadabe mai ritaya ne ya sanya hannu kan sanarwar a madadin Kwamitin Amintattu na ƙungiyar.
Taken taron shi ne, “Daga Sadaukarwa Zuwa Dabarun Aiki: Farfaɗo Da Hangen Janar Hassan Usman Katsina Kan Samar Da Arewa Mai Wadata.” An fitar da sanarwar matsayar taron a ƙarshen mako.
Taron ya haɗa manyan ’yan siyasa, sarakunan gargajiya, malaman addini, masana da sauran masu ruwa da tsaki daga sassa daban-daban. Tsohon Shugaban Hafsan Sojojin Nijeriya, Manjo-Janar Alwali Kazir mai ritaya, ne ya jagoranci taron, yayin da Alhaji Ibrahim Masari ya wakilci Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.
Shugaban ƙungiyar Dattawan Arewa, Farfesa Ango Abdullahi, ya gabatar da wani rahoto na musamman, yayin da Dakta Usman Bugaje na Arewa Research Development Project ya gabatar da babban jawabin taron. Farfesa Siddiƙue Abubakar Mohammed na Cibiyar Bincike da Horarwa kan Ci Gaba da ke Zariya ne ya jagoranci tattaunawa kan jawabin.
Taron ya ce bayan shafe shekaru ana tattauna matsalolin da ke addabar Arewa, lokaci ya yi da yankin zai daina tsaya wa kan gano matsaloli kawai, ya koma ɗaukar matakan da za su kawo sauyi a aikace.
Daga cikin manyan ƙalubalen da aka bayyana akwai rashin tsaro, raba manoma da gonakinsu sakamakon hare-hare, ci gaba da tsarin almajiranci da kuma yawan yaran da ba sa zuwa makaranta.
Masu halartar taron sun kuma nuna damuwa kan yadda darajar wasu muhimman al’adun Arewa ke raguwa, inda suka ce dukiya ta fara samun fifiko a kan ilimi wajen tantance wanda ya dace da jagoranci.
Sun kuma ce abin damuwa ne yadda a wasu lokuta ake bai wa masu hannu cikin cin hanci da rashawa da kuma masu yi wa shugabanni biyayya ba tare da tunani ba, ƙima fiye da mutanen da suka kasance masu gaskiya da ɗabi’a nagari.
Taron ya soki yadda ake kashe ɗimbin dukiyar al’umma wajen shagulgulan aure, suna da sauran bukukuwa masu tsada, yana mai cewa irin wannan kuɗi za a iya karkatar da shi wajen rage talauci da gudanar da ayyukan ci gaban al’umma.
Haka kuma, taron ya nuna damuwa kan yadda ake yin sakaci da ilimin ’ya’ya mata, inda ya jaddada cewa ya kamata a ba su ilimi da dabarun sana’a da za su taimaka musu wajen dogaro da kansu da kuma kula da iyalansu.
Sanarwar ta kuma yi Allah-wadai da yadda cin hanci da rashawa ya yi katutu a fannoni daban-daban, ciki har da wasu daga cikin shugabannin addini, tana mai gargaɗin cewa hakan na taimakawa wajen rushe muhimman zabi’un gargajiya kamar gaskiya, mutunci, girmamawa, sadaukarwa, adalci, kiyaye lokaci da kuma jajircewa wajen gudanar da aiki.
Wani babban abin da taron ya nuna damuwa a kai shi ne rashin ingantaccen tsarin ƙididdigar yawan jama’a.
A cewar mahalarta taron, Arewa ba ta da cikakkiyar hanyar bibiyar yawan mutanen da ake haifa da waɗanda ke mutuwa, masu aure ko waɗanda ke ƙaura daga wani wuri zuwa wani. Wannan, a cewarsu, na ƙara wahalar da tsarin tsara manufofin ci gaba bisa sahihan bayanai.
Masu ruwa da tsakin sun kuma ɗora alhakin ci gaba da raunin Arewa kan rikice-rikicen da ke tsakanin shugabannin siyasa, sarakunan gargajiya da malaman addini.
Sanarwar ta ce, “Dole Arewa ta samu manufa guda wajen samar da ci gabanta,” tana mai cewa ba za a samu gagarumin ci gaba ba matuƙar shugabannin yankin ba su haɗa kai wajen tunkarar matsalolin da ke gabansu ba.
Taron ya kuma soki yadda wasu ’yan siyasar Arewa suka mayar da hankali kan kamfen da yawan furuci ba tare da ɗaukar matakan da suka dace ba, yana mai cewa lokaci ya yi da za a sauya gadon da Janar Hassan Usman Katsina ya bari zuwa ayyukan zahiri da za su amfani al’umma.
Haka kuma, mahalarta taron sun buƙaci a sake duba dabarun da ake amfani da su wajen yaƙi da rashin tsaro, suna cewa hanyoyin da aka fara amfani da su tun daga shekarar 2009 ba su samar da sakamakon da ake fata ba.
ɗaya daga cikin muhimman batutuwan da taron ya fi mayar da hankali a kai shi ne matsalar almajirai, wadda mahalarta suka bayyana a matsayin ɗaya daga cikin manyan barazanar da ke fuskantar jarin ɗan Adam na Arewa, tattalin arzikinta, tsaro, zaman lafiyar al’umma da kuma ci gaba mai ɗorewa.
ƙungiyar NEVDI ta ƙuduri aniyar samar da wani tsari na musamman da zai taimaka wajen fitar da yaran almajirai daga tituna, tare da samar musu da ilimi mai ma’ana da damar samun kyakkyawar makoma.
A ƙarƙashin shirin, za a tattara attajirai da masu hannu da shuni daga jihohin Arewa waɗanda suke da niyyar taimakawa wajen ganin an aiwatar da shirin. Haka kuma, za a samar da tsarin bai ɗaya da za a bi wajen aiwatar da shirin, yayin da kwamitin amintattu zai riƙa kula da ayyukansa.
Sai dai taron ya jaddada cewa nasarar shirin ba za ta tsaya kawai ga cire yaran daga tituna da kai su makarantu ba. Ya ce, babban burin shi ne tabbatar da cewa kowane yaro, ba tare da la’akari da jinsinsa, inda yake zaune, nakasa, yanayin tattalin arzikinsa ko irin tsarin ilimin da ya saba da shi ba, ya samu ilimi mai amfani, ƙwarewa da dabarun da za su ba shi damar zama ɗan ƙasa mai amfani ga kansa da al’ummarsa.
Sanarwar ta yi gargaɗin cewa ba za a iya magance matsalar almajirai da tarukan tattaunawa, shirye-shiryen talabijin da rediyo, ƙananan ayyukan da ba su da alaƙa da juna ko kuma shirye-shiryen wucin gadi kawai ba.
Maimakon haka, ta buƙaci a samar da ɗorewar hanya mai haɗin gwiwa wadda za ta haɗa gwamnatoci, abokan hulɗar ci gaba, ƙungiyoyin farar hula, al’ummomi, masu hannu da shuni, daidaikun mutane da kuma kamfanoni masu zaman kansu.
NEVDI ta yi alƙawarin mayar da matsayar taron zuwa “mafita ta zahiri, wadda za a iya gwadawa tare da faɗaɗa ta” domin magance matsalolin da yankin ke fuskanta.
