Hukuma ta kashe gobara sama da 100 tsakanin Janairu da Satumba a Nasarawa

Spread the love

Daga JOHN D. WADA, a Lafiya

Hukumar kashe gobara ta tarayya reshin jihar Nasarawa tace ta amsa kira sama da 100 na gaggawa tsakanin watan Janairu zuwa Satumba na shekarar 2026 kaɗai.

Shugabar hukumar ta jihar Mrs. Eno Nwachukwu ce ta bayyana hakan a ƙarshen makon da ya gabata a Lafiya babban birnin jihar yayin wani gangamin wayar da kai da aka shirya gabanin watannin Ember.

Gangamin wanda aka yi da taken “Tsaron Gobara, ƙaura a lokacin gaggawa da horon yadda ake kashe gobara da ba da agajin gaggawa,” an shirya shi ne domin ilimantar da jama’a kan hanyoyin kariya daga gobara da yadda ake ba da agaji a lokacin gaggawa.

A cewar Nwachukwu kiran sun haɗa da ɓarkewar gobara da sauran ayyukan ceto a faɗin jihar wanda ya kai ga ceto rayuka da dukiyoyi da suka kai miliyoyin Naira.

Tace rukunin ya samu nasarar amsa dukkan kiran da kashi 100 cikin 100 a cikin wannan lokaci.

“Tun daga farkon wannan shekara mun samu kira sama da 80 zuwa 100 kan gobara. Ina godiya ga Allah cewa babu kiran gobara da muka kasa shawo kansa a cikin wannan lokaci. Idan kuka kira mu akan lokaci ku ɗauka cewa an gama, babu wani gini da gobara ta cinye gaba ɗaya. Mun samu nasarar shawo kan dukkan lamuran,” in ji ta.

Nwachukwu ta kuma bayyana cewa gangamin wayar da kan na watannin Ember ya zama wajibi saboda yawaitar faruwar gobara a wannan lokaci wanda galibi sakamakon sakaci ne kamar rashin kashe kayan lantarki yayin barin gida da kuma yawan lodin na’urori a madafun wuta guda.

Tace wannan shiri na daga cikin matakan kariya domin jawo hankalin jama’a kan yadda za su kare kansu daga ɓarkewar gobara da kuma yadda za su sarrafa lamarin kafin jami’an kashe gobara su iso.

By ukarofi

Leave a Reply