Dag ABUBAKAR A BOLARI Gombe
Wata ƙungiyar siyasa mai suna Nigeria Forward, ta yi kira ga masu ruwa da tsaki a siyasar Arewacin Najeriya da kada su yi watsi da tsarin karɓa-karɓa na shugabancin ƙasa tsakanin Arewa da Kudu.
Ƙungiyar ta ce ya kamata Arewa ta mutunta fahimtar da aka cimma tun bayan komawar dimokuradiyya a 1999, ta hanyar bai wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu damar kammala wa’adinsa na shekaru takwas kafin a nemi dawo da shugabancin ƙasa Arewa.
Mataimakin jagoran ƙungiyar, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, wanda shi ne kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida na Jihar Kano, ya bayyana hakan ne yayin bikin ƙaddamar da ƙungiyar a hukumance.
Waiya ya ce tun bayan komawar Najeriya tsarin dimokuradiyya a 1999, tsarin sauya shugabanci tsakanin Arewa da Kudu ya kasance wani muhimmin abu wajen ƙarfafa haɗin kan ƙasa da daidaita rabon mulki.
Ya ce ƙoƙarin dawo da mulki Arewa a 2027, bayan wa’adi ɗaya kacal, na iya kawo cikas ga wannan fahimta tare da sake tayar da batun rabuwar kai a siyasar ƙasar.
“Bai kamata Arewa ta nemi karɓar shugabancin ƙasa a 2027 ba bayan shekaru huɗu kacal na gwamnatin yanzu ba. Ya kamata a bar Tinubu ya kammala shekaru takwas, domin gwamnati ta samu damar ƙarfafa manufofi da shirye-shiryen da ta fara,” in ji shi.
Ya kuma yi kira ga ‘yan siyasar Arewa da su fifita haɗin kan ƙasa da ci gaban Najeriya a kan muradun siyasar zaɓe.
Waiya ya ce gwamnatin Tinubu ta gaji manyan matsalolin tattalin arziki da tsaro a shekarar 2023, yana mai cewa wasu daga cikin matakan da ta ɗauka sun fara sauya alkiblar ƙasar.
Ya ambaci cin gashin kan ƙananan hukumomi, ƙarin kuɗaɗen da ke zuwa ga gwamnatocin jihohi da ƙananan hukumomi, da kuma shirin kafa ‘yan sandan jihohi a matsayin wasu daga cikin gyare-gyaren da zai iya inganta shugabanci da tsaro.
Ya bayyana cewa Jihar Kano ta riga ta kafa kwamitin aiwatar da tsarin ‘yan sandan jiha, wanda ya ce zai taimaka wajen samar da ayyukan yi da inganta tsaro idan aka kammala aiwatar da shi.
A nasa jawabin, Ministan Kirkire-kirkire, Kimiyya da Fasaha, Dakta Kingsley Tochukwu Udeh, wanda shi ma ɗaya ne daga cikin waɗanda suka jagoranci ƙaddamar da kungiyar, ya ce gyare-gyaren gwamnatin tarayya na da nufin bunƙasa ababen more rayuwa, samar da ayyukan yi da ƙara bunƙasa tattalin arziki.
Udeh ya ce bai kamata a mayar da batun ci gaban Najeriya, musamman na Arewa, zuwa kalaman siyasa kawai ba, sai an duba ayyukan da ake gudanarwa, matsalolin da suke magancewa da kuma al’ummar da za su amfana.
Ya ce hanyoyi ya kamata su haɗa manoma da kasuwanni, yayin da layin dogo zai taimaka wajen rage kuɗin jigilar kayayyaki.
Ya bayyana tsarin ci gaban gwamnatin da cewa: “Daga gyare-gyare zuwa ababen more rayuwa, daga ababen more rayuwa zuwa haɗin kai, daga haɗin kai zuwa samar da kayayyaki, daga samar da kayayyaki zuwa ayyukan yi, sannan daga ayyukan yi zuwa wadata.”
Udeh ya kuma yi kira ga ‘yan Najeriya da su goyi bayan sake zaɓen Tinubu a 2027 domin ci gaba da gyare-gyaren da gwamnatin ta fara.
Ya buƙaci mambobin Nigeria Forward da su gina ayyukansu bisa hujjoji, haɗin kai, ƙirƙire-ƙirƙire da kishin ƙasa, domin tabbatar da taken ƙungiyar na “Tare za mu kai Najeriya gaba.” ta jira har 2031 kafin neman mulki – Nigeria Forward
