Daga JAMIL GULMA a Kebbi
Alhaji Abdulrazak Muhammed daga ƙaramar hukumar Argungu ɗaya daga cikin manyan mashawartan gwamna Malam Nasir Idris ya sanar da ajiye muƙamin sa tare da barin jam’iyyar APC.
Ya bayyana haka ne a gidan sa da ke Argungu a wani taron manema labarai da ya shirya ranar Laraba ɗin nan.
Alhaji Abdulrazak Muhammed wanda tsohon kwamishinan dindindin kan harkokin majalisar dokokin jihar ne ya bayyana cewa ya yanke shawarar barin jam’iyyar APC ne saboda rashin yin abinda ya kamata tun kama daga yi wa talakawa ayyukan cigaba musamman abinda ya shafi tsaro ya zuwa yin ko-oho da yan siyasa da suka yi ruwa suka yi tsaki wajen ganin an kafa wannan gwamnatin.
Ya ƙara da cewa duk wanda ya riƙa irin muƙamin sa ba shakka yana da dubban magoya baya amma duk aka yi watsi da su, saboda haka ya nemi duk magoya bayan sa da su fice daga jam’iyyar APC su koma jam’iyyar ADC daga yau 23 ga watan Satumba.
Ya kuma bayar da tabbacin bayar da gudummawar da duk zai iya wajen ganin jam’iyyar ADC ta cimma nasara tun daga matakin shugaban ƙasa zuwa Kansila in sha Allahu.
