Daga JOHN WADA a Lafia
Yayin da Jihar Nasarawa ke cigaba da shirin cika shekaru 30 da kafuwa, mataimakin gwamnan jihar Dakta Emmanuel Akabe ya yi kira ga mazauna jihar da su rungumi zaman lafiya da haɗin kai da kuma ɗaukar nauyin makomar jihar tare.
Akabe wanda shi ne shugaban kwamitin shirye-shiryen bikin cika shekaru 30 ɗin yayi wannan kiran ne a ranar Alhamis yayin wani taron manema labarai a Lafia.
Ya bayyana cewa an ƙirƙiro jihar Nasarawa a shekarar 1996 a zamanin mulkin soja na marigayi Janar Sani Abacha kuma bikin cika shekaru 30 ɗin ya ba da damar yin murna da kuma yin nazari mai zurfi.
A cewarsa, Gwamna Abdullahi Sule ya amince da gudanar da bikin a matsayin wata hanya ta karrama tafiyar da jihar ta yi zuwa yanzu, da kuma yaba wa waɗanda suka ciyar da jihar gaba, da duba nasarori da ƙalubalen da aka fuskanta, da kuma sabunta ƙudurin gina jiha mai haɗin kai da cigaba.
A wani ɓangare na shirye-shiryen, mataimakin gwamnan ya kuma yo amfani da damar inda ya sanar cewa an kuma gayyaci wasu fitattun ‘yan Najeriya guda biyu a matsayin masu gabatar da laccoci na musamman wato tsohon Shugaban hukumar zaɓe na ƙasa INEC, Farfesa Attahiru Jega, zai yi lacca akan taken “Jihar Nasarawa a Shekara 30: Daga Kafawa zuwa Sauyi,” yayin da Bishop Matthew Kukah kuma zai gabatar da lacca kan “Haɗin kai a cikin bambance-bambance: Shekaru 30 na gina Jihar Nasarawa mai haɗin kai – Matsaloli da ƙalubale da makoma.”
Akabe ya kuma jaddada cewa bikin ya wuce kawai cika kalandar shekaru.
“Wannan biki game da mutanenmu ne, al’adunmu da kuma asalinmu na bai ɗaya. Game da yaba wa magabatanmu ne da tsofaffi da gwamnonin dake kan mulki da sarakunan gargajiya da mata da matasa da ma’aikatan gwamnati da kowane ɗan ƙasa da ya bayar da gudummawa wajen cigaban Nasarawa,” in ji shi.
Yace taron zai kuma nuna irin cigaban da gwamnatocin baya suka samu a fannonin ilimi da kiwon lafiya da ababen more rayuwa da bunƙasa ƙarfin ɗan Adam da tsaro da kasuwanci da kuma zuba jari.
“Wannan ita ce jiharmu da tarihinmu da makomarmu ta bai ɗaya. Dole ne mu yi bikin cika shekaru 30 na Nasarawa da godiya ga jiya da alfahari da yau da kuma fatan samun kyakkyawar gobe,” in ji Akabe.
