Rashin halartar Gwamna Abba taron MAN ya bada mamaki – Mahalarta

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano

Ganin yadda Kano ta zama ɗaya daga cikin manyan cibiyoyin kasuwanci da masana’antu a Nijeriya, musamman a Arewacin ƙasar, rashin halartar gwamnan jihar ta Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ko wani wakilinsa a taron shekara-shekara na ƙungiyar Masu Masana’antu ta Nijeriya (MAN), ya jawo tambayoyi da mamaki daga akasarin mahalarta wannan gagarumin taron.

Masu masana’antu da kamfanoni a Jihar Kano na ci gaba da ƙoƙarin ganin jihar ta riƙe matsayinta a fannin masana’antu, duk da matsalolin da suka haɗa da rashin wadataccen wutar lantarki, tsadar man gas, yawan haraji da sauran ƙalubalen da ke addabar harkokin kasuwanci da masana’antu a ƙasar.

Duk da waɗannan ƙalubale, ƙungiyar MAN ta ci gaba da gudanar da ayyukanta a Kano, lamarin da ya sa wasu mahalarta taron suka yi mamakin rashin ganin Gwamna Abba Kabir Yusuf ko wani wakilinsa a wajen taron. Haka kuma, ba a ga Mai Garin Kano ko wani wakilinsa ba, duk da cewa wata majiya a wajen taron ta ce an gayyaci shugabannin.

Taron MAN na shekara-shekara na daga cikin hanyoyin da ƙungiyar ke amfani da su wajen baje kolin kayayyakin da kamfanoni da masana’antunta ke samarwa, tare da wayar da kan al’umma kan irin gudunmawar da suke bayarwa wajen bunƙasa tattalin arziki da rage wa gwamnati nauyi ta hanyar samar da ayyukan yi ga miliyoyin matasa.

A wannan karon ma, MAN ta gudanar da taronta kamar yadda ta saba a kowace shekara, inda kamfanoni da masana’antu daban-daban suka baje kolin kayayyakin da suke samarwa. Kamfanin ASPIRA, ƙarƙashin jagorancin ɗaya daga cikin manyan jami’ansa, Alhaji Haruna Haske, ya halarci bajakolin, yayin da Malam Mustapha Bala Abubakar, ɗaya daga cikin manyan jami’an kamfanin SUPER KILL, mai sarrafa maganin sauro da sauran kayayyakin amfani na yau da kullum, shi ma ya wakilci kamfaninsa.

Taron ya samu halartar wasu shugabanni da manyan jami’an kamfanoni da masana’antu daga Kano da Jigawa, da kuma sauran manyan baƙi, ciki har da Mai Girma Makama Alhaji Muhammad Tofa, wanda aka fi sani da ɗan Adala, da Shugaban MAN na Kano, Alhaji Madugu, da sauran mahalarta.

Da yake magana a ƙarshen taron, Alhaji Bello Muhammad Tofa, shugaban ƙungiyar MAN mai kula da shiyyar masana’antu ta Bompai, Kano, kuma shugaban MAN a Jihar Jigawa, ya ce babban kiran da suke yi wa gwamnati a kowane mataki shi ne a yi la’akari da irin gudunmawar da masana’antu ke bayarwa ga tattalin arzikin ƙasa.

Ya ce a halin yanzu akwai kamfani guda da ke ɗaukar matasa sama da 20,000 aiki, yayin da wasu ke ɗaukar 10,000, 15,000 da dubban sauran ma’aikata a yankunan Kano da Jigawa. Saboda haka, ya ce suna buƙatar gwamnati ta sassauta haraji tare da samar da tsarin haraji guda ɗaya da ba zai yi wa kamfanoni da masana’antu nauyi ba.

Alhaji Tofa ya kuma yi kira da a daina sanya hukumomi masu tabbatar da bin ƙa’ida a fannoni daban-daban su riƙa ɗora wa kamfanoni harajin da suke biya duk shekara, yana mai bayar da misali da NAFDAC da SON. A cewarsa, irin waɗannan kuɗaɗe na ƙara wa kamfanoni da masana’antu cikas wajen gudanar da ayyukansu, musamman kasancewar ba hukumomin da ke karɓar harajin shigo da kaya kamar Hukumar Kwastam ta Nijeriya (NCS) ba.

By ukarofi

Leave a Reply