Taron mauludi babbar makaranta ce mai zurfi – Sheriff Haruna

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano

Daya daga cikin jagororin Sharifan Nijeriya, Alhaji Sheriff Haruna Sheriff Abba Garin Ali, na ƙaramar hukumar Garko a Jihar Kano, ya bayyana cewa tarukan Maulidi da al’ummar Musulmi ke gudanarwa a kowace shekara wata babbar makaranta ce mai zurfi da ke bayar da ilimi da fa’ida ga al’umma.

Sheriff Haruna ya bayyana cewa tun daga shigowar watan Rabi’ul Awwal har zuwa watannin da ke biyo baya, ana gudanar da tarukan Maulidi a masallatai, zawiyoyi, gidajen ’yan Muhammadu, makarantu na addini da na zamani, ma’aikatu, kasuwanni da sauran wurare masu albarka.

Ya ce a irin waɗannan taruka ana gayyatar manyan malamai, masana da sauran bayin Allah domin gabatar da jawabai kan tarihin Manzon Allah (SAW), iyalansa, sahabbansa da sauran batutuwa masu alaƙa da rayuwarsa. Haka kuma, a makarantu na addini da sauran wurare, ɗalibai kan gabatar da karatu kamar Sira da sauran darussa.

Ya ƙara da cewa sau da yawa mutum kan ji wani sabon bayani a wajen taron Maulidi wanda bai taɓa saninsa ba, ko da yake yana karatu a makaranta. A cewarsa, wannan na nuna irin babbar fa’idar da tarukan Maulidi ke da ita wajen ƙara ilimi da kuma nuna soyayya ga Manzon Allah (SAW).

Sheriff Haruna ya kuma yi nasiha ga masu shirya tarukan Maulidi da su tsarkake niyyarsu, su yi abin da suke yi domin Allah, tare da guje wa duk wani abu da Allah da Manzonsa suka haramta ko suka ƙi. Ya ce duk aikin alheri na iya fuskantar ƙalubalen Shaidan ta hanyar son zuciya, riya ko wasu abubuwa makamantansu, don haka ya yi addu’ar Allah Ya datar da Musulmi baki ɗaya.

A ƙarshe, Sheriff Haruna Abba Garin Ali ya yi kira ga wasu malamai da su ƙara mai da hankali wajen koyar da mutane addini gwargwadon fahimtarsu, tare da guje wa koyarwar da ba ta da amfani ko kuma wadda ka iya jefa mutane cikin ruɗani a addini.

Ya ce Musulmi ba sa son jin duk wani karatu ko bayani da zai taɓa darajar Manzon Allah (SAW) ko mutuncin iyalansa, yana mai jaddada buƙatar koyar da addini cikin hikima da kiyaye mutuncin Manzon Allah da Ahlul Baiti.

By ukarofi

Leave a Reply