Marasa lafiya biyu sun rasu a Babban Asibitin Ƙasa bayan karɓar allurar Ceftazidime

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Babban Asibitin Ƙasa a Abuja, ya tabbatar da mutuwar wasu marasa lafiya guda biyu bayan shiga halin tsanani sakamakon zargin tasirin wata allura ta Fortcef, daga dangin sinadarin Ceftazidime.

Asibitin ya sanar da haka ne a wata takarda da ya fitar mai ɗauke da 10 ga Satumba, 2026 daga Daraktan Harkokin Lafiya kuma Shugaban Kwamitin Shawarwarin Lafiya, Dakta O. Lawal.

Wannan al’amari ya sanya asibitin ya ƙarfafa matakan sanya ido kan magungunan Ceftazidime da ake shigowa da su daga wajen asibitin musamman allurar Forcef mai nauyin gram 1.

A cewar sanarwar, kwamitinta tantance magani ne ya gano al’amarin bayan faruwar wasu ababe akan marasa lafiya biyun. Asibitin ya bayyana cewa ba sa cikin mawuyacin hali gabanin a tsira musu allurar sinadarin. Akan haka ne hukumar gudanarwar asibitin ya umarci sashen lafiya da ya ƙarfafa matakan sanya ido kan dukkan wani sinadari da ya shafi Ceftazidime da aka shigo da shi daga wajen asibitin.

Maganin da al’amarin ya shafa shi ne mai ɗauke da lambar aiki kamar haka: PEZIE001, wanda aka buga a watan Mayun 2025 kuma aka sa aikinsa zai ƙare a watan Afrilun 2028. Rajistarsa ta hukumar NAFDAC ita ce C4-0247.

Tuni dai asibitin ya ankarar da jami’an lafiya da kuma aike wa NAFDAC rahoton faruwar al’amarin. A yanzu dai ana cigaba da gudanar da bincike domin gano haƙiƙanin yadda al’amarin ya faru da kuma dalilan da suka sabbaba faruwarsa.

By Babaji

Leave a Reply