Jiragen kasuwanci za su fara tashi gobe a Gusau yayin bikin cikar Zamfara 30

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Jihar Zamfara za ta cika shekaru 30 da kafuwa gobe, 1 ga Oktoba, tare da ƙaddamar da zirga-zirgar jiragen sama na kasuwanci zuwa Gusau a matsayin babban abin da zai haskaka bikin.

Sakataren gwamnatin Jihar, Abubakar Nakwada, ya bayyana haka a wani taron manema labarai yau Laraba.

Ya bayyana cewa bikin cika shekaru 30 ɗin ba biki ne kawai ba, illa dama ce ta yin nazari kan shekaru talatin na juriya da kuma tsara sabuwar hanya ga sabuwar Zamfara.

Nakwada ya ce shekaru ukun da suka gabata a ƙarƙashin Gwamna Dauda Lawal sun shaida samun sauye-sauye da nufin magance matsalolin ci gaba da suka dade ana fama da su.

Ya bayyana tsaro a matsayin ginshiƙin wannan sauyi, inda ya ce gwamnati ta tallafa wa sojoji, ‘yan sanda, DSS da NSCDC da motocin aiki, motocin sulke, jiragen leƙen asiri marasa matuƙi (drones) da babura.

A cewarsa, kafa rundunar Community Protection Guards a matsayin Wani aikin jami’an tsaro na yau da kullum ta hanyar samar da bayanan sirri daga matakin al’umma da sanin yadda yankuna suke.

Ya ƙara da cewa gyare-gyaren tsarin mulki ya kasance babban ginshiƙi, inda gwamnatin ta biya bashin albashin da ta gada domin dawo da ƙwarin gwiwar aikin gwamnati, ta sake fasalin ma’aikatu da hukumomi (MDAs), tare da zuba jari a kayayyakin ICT domin tabbatar da gwamnatin e-governance da tafiyar da harkoki bisa bayanai.

A cewarsa, don haka sauyi yana faruwa ta fuskoki biyu wajen samar da kayayyakin more rayuwa da kuma zamanantar da tsarin gudanarwa.

A fannin ci gaban dan Adam, Nakwada ya ce gyare-gyare a fannin ilimi sun wuce gyaran ajujuwa, an koma ga sake ginawa da kuma samar da cikakkun kayayyakin karatu domin ƙarfafa shigar yara makaranta, ci gaba da zama da kuma kammalawa tare da rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta.

Ya ce irin wannan tsari ya shafi asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya na farko, yayin da a fannin noma, wanda aka gina kan taken “Farming is Our Pride” (Noma Abin Alfaharinmu), ya ce gwamnatin jihar ta raba ingantattun iri, takin zamani tare da sayo daruruwan taraktoci kwanan nan domin sauya sheka daga noman gargajiya zuwa na zamani yayin da tsaro ke inganta.

SSG ɗin ya ce sauyi a fannin tattalin arziki ya mayar da hankali ne kan tsara harkokin hakar ma’adinai, aiwatar da ka’idoji da kuma karfafa sarrafa ma’adinai a cikin gida da kuma kara musu daraja domin samar da ayyukan yi da kuma kuma kula dukiyar jihar.

By ukarofi

Leave a Reply