Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Ƙungiyar marubuta labarin wasanni ta ƙasa reshen Jihar Katsina (SWAN) ta kammala shirye shiryen gudanar da gasar ƙwallon ƙafa tsakanin ma’aikatun, hukumomi gwamnati da ke faɗin jihar.
Gasar mai taken (Dikko Raɗɗa Inter-Ministrial Football Competition 2026) a turance, an shirya ta ne domin ƙarfafa kyakkyawar alaƙa da haɗin kai tsakanin ma’aikatan gwamnatin, tare da ƙarfafa lafiyar jiki,aiki da kyakkyawar mu’amala a tsakanin ma’aikatan gwamnatin.
A cewar ƙungiyar (SWAN), gasar za ta bai wa ma’aikata daga ma’aikatu daban daban da hukumomi damar haɗuwa ta hanyar wasanni, domin ƙarfafa haɗin kai da zumunci a tsakaninsu,ba tare da la’akari da nauyin ayyukan da suke gudanarwa a hukumance ba.
Katsina SWAN ta bayyana gasar a matsayin wata muhimmiyar sabuwar kafa,kasancewar irinta ce ta farko tun bayan komawar mulkin dimokuraɗiyya a Jihar Katsina.
Haka kuma Katsina SWAN ta nuna godiyarta ga gwamnatin Malam Dikko Umaru Raɗɗa bisa goyon bayan da take bai wa ƙungiyar da kuma ƙoƙarinta na bunƙasa rahotannin wasanni da harkokin su a fadin jihar.
Ƙungiyar ta ce ana sa ran gasar za ta ƙara ƙarfafa kyakkyawar alaƙa tsakanin kafafen yaɗa labarai,hukumomin Gwamnati da masu ruwa da tsaki a harkokin wasanni a Jihar Katsina.
