Shettima ya nemi goyon bayan ‘yan Kannywood don tabbatar da nasarar Tinubu a 2027

Spread the love

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima, ya buƙaci ƙwararrun ’yan mawaƙa da ‘yan fim na Arewa da su mara wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya a zaɓen 2027, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen tabbatar da haɗin kan ƙasa da ci gabanta.

Shettima ya bayyana hakan ne ranar Laraba, lokacin da ya karɓi tawagar Shugabanni da mambobin ƙungiyar Triple-R For Renewed Hope a ofishin yaƙin neman zaɓen APC da ke Abuja.

Mataimakin shugaban ƙasar ya ce gwamnatin Tinubu tana aiwatar da manufofin da za su bunƙasa masana’antar Kannywood da suka haɗa da tallafa wa masu shirya fina-finai, mawaƙa da sauran masu sana’o’in kirkire-kirkire. Ya kuma bayyana cewa Arewa za ta amfana da shirye-shiryen bunƙasa tattalin arzikin ƙasa ta hanyar fasaha, tare da samar da ayyukan yi da kiyaye al’adu.

A nasa jawabin, Darakta-Janar na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa, Sanata Abdulaziz Yari, ya ce nasarar Tinubu a zaɓen 2027 za ta dogara ne da ayyuka da nasarorin gwamnatinsa, inda ya buƙaci masu ruwa da tsaki su yi la’akari da abubuwan da ke kasa. Tsohon gwamnan Katsina, Aminu Bello Masari, da tsohon gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, sun kuma gode wa tawagar bisa goyon bayansu, tare da kira da a tabbatar da adalci, daidaito da haɗa kan al’umma.

Shugaban ƙungiyar Triple-R For Renewed Hope, Alhaji Dauda Kahutu Rarara, ya bayyana aniyar ƙungiyar ta tallafa wa Tinubu da sauran ’yan takarar APC a zaɓen 2027. Ya ce ’yan masana’antar nishaɗi da fasaha a Arewa sun haɗa kai wajen wannan manufa, sannan ya nemi gwamnatin tarayya ta ƙara tallafa wa masana’antar ta hanyar samar da kayayyakin more rayuwa da horar da matasa masu tasowa a fannin.

By Babaji

Leave a Reply